- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Theft and Thieves
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Ba za ka yi sata ba.
“Duk wanda ya saci mutum ya sayar da shi, ko kuwa aka iske shi a hannunsa, lalle kashe shi za a yi.
“In mutum ya saci saniya ko tunkiya ya yanka, ko ya sayar, zai biya shanu biyar, a maimakon saniyar da ya sata, ko kuma tumaki huɗu, maimakon tunkiyar da ya sata.
“In aka iske ɓarawo yana cikin ƙoƙarin shiga yă yi sata, aka buge shi har ya mutu, to, ba za a nemi alhakin jininsa daga wurin kowa ba;
amma in ya faru bayan wayewar gari, to, za a nemi alhakin jinin ɓarawon a hannun wanda ya bugi ɓarawon. “Ɓarawon da aka kama da abin da ya sata, dole yă yi cikakkiyar ramuwa, amma in ba shi da kome, dole a sayar da shi a biya abin da ya sata.
In an sami dabbar, ko saniya, ko jaki, ko tunkiya da ya sata da rai a hannunsa, dole ɓarawon yă biya taran da za a ci shi, sau biyu na kowane ɗaya.
“In mutum ya ba da jaki, ko saniya, ko tunkiya, ko kowace dabba wa maƙwabcinsa ajiya, sai abin ya mutu, ko ya ji rauni, ko an ɗauke shi, in ba shaida,
rantsuwa ce za tă raba tsakaninsu a gaban Ubangiji cewa babu hannunsa a dukiyar maƙwabcinsa. Mai dukiyar kuwa zai yarda da rantsuwar, ba za a bukaci wanda aka bai wa amanar yă biya ba.
Amma idan satan dabbar ce aka yi, dole wanda aka bai wa ajiyar yă biya mai dabbar taran da aka ci masa.
In naman jeji ne ya kashe ta, zai nuna gawar don shaida, ba za a kuwa sa maƙwabcin yă biya abin da naman jeji ya kashe ba.
“In mutum ya yi aron dabba daga wurin maƙwabcinsa, sai dabbar ta ji rauni ko ta mutu, yayinda mai shi ba ya nan, dole wanda ya yi aron dabbar yă biya.
Amma idan mai dabbar yana a wurin, wanda ya karɓa aron, ba zai biya kome ba. In an yi hayar dabbar ce, to, kuɗin da aka biya na hayar zai zama a madadin rashin.
“In wani ya yi zunubi bai kuma yi aminci ga Ubangiji ba, wato, ta wurin yin wa abokin zamansa karya game da ajiyar da abokin ya ba shi amana, ko a kan wani alkawarin da suka yi wa juna, ko kuwa a kan yă cuci abokin,
ko kuma idan ya sami abin da ya ɓace amma ya yi ƙarya cewa bai samu ba. Ko ya yi rantsuwar ƙarya a kan duk irin abubuwan da akan aikata na laifi,
sa’ad da mutum ya yi irin laifin nan, ya kuwa tabbata mai laifi ne, to, sai yă komar da abin da ya ƙwace, ko abin da ya samu ta hanyar zalunci, ko abin da aka ba shi ajiya, ko abin da ya tsinta.
Zai mai da abin da ya yi rantsuwar ƙarya a kai. Zai mayar wa mai abin da abinsa a yadda yake, har yă ƙara kashi ashirin bisa ɗari na abin. A ranar da zai yi hadaya don laifinsa, a ranar ce zai mayar wa mai abin da abinsa.
A matsayin hakki kuwa, dole yă kawo wa firist, wato, ga Ubangiji, hadaya rago marar lahani kuma wanda aka kimanta tamaninsa daga garke don laifinsa.
Ta haka firist zai yi kafara dominsa a gaban Ubangiji, za a kuwa gafarta masa irin laifin da ya yi.”
“ ‘Kada ku yi sata. “ ‘Kada ku yi ƙarya. “ ‘Kada ku ruɗe juna.
“ ‘Kada ku zalunci maƙwabcinku, ko ku yi masa ƙwace. “ ‘Kada ku riƙe albashin ma’aikaci yă kwana.
Kada ka yi sata.
In kun shiga gonar inabin maƙwabcinku, za ku iya cin inabin da kuke so, amma kada ku sa wani a kwandonku.
In kun shiga gonar hatsin maƙwabcinku, za ku iya murmure tsabar da hannuwanku, amma kada ku sa lauje ku yanka hatsinsa da yake tsaye.
Sa’ad da kuka ga ɓarawo, kukan haɗa kai da shi; kukan haɗa kai da mazinata.
Kada ku dogara a kan ƙwace ko yin fariya a kayan sata; ko arzikinku ya ƙaru, kada ku sa zuciyarku a kansu.