Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Theft and Thieves

63 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”

  2. Sai ya shiga filin haikali, ya fara korar masu sayar da kaya.

  3. Ya ce musu, “A rubuce, yake cewa, ‘Gidana, zai zama gidan addu’a,’amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’ ”

  4. “Gaskiya nake gaya muku, mutumin da bai shiga inda ake ajiye garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya hau ta katanga, ɓarawo ne, ɗan fashi kuma.

  5. to, kai mai koya wa waɗansu, ba kanka kake koya wa ba? Kai da kake wa’azi kada a yi sata, kana sata?

  6. Umarnan nan, “Kada ka yi zina.” “Kada ka yi kisankai.” “Kada ka yi sata.” “Kada kuma ka yi ƙyashi.” Da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”

  7. Amma ga shi ku da kanku kuna cuta, kuna kuma zamba, har ma ga ’yan’uwanku ne kuke yi wannan.

  8. ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah.

  9. Duk wanda yake sata, sai yă daina sata, dole kuma yă yi aiki, yă yi wani abu mai amfani da hannuwansa, don yă sami abin da zai iya raba da masu bukata.

  10. kada kuma su yi musu sata, sai dai su nuna za a iya amince da su sosai, don ta kowace hanya su sa koyarwa game da Allah Mai Cetonmu ta zama abin ɗaukan hankali.

  11. In kuna shan wahala, kada yă zama don ku masu kisankai ne ko ɓarayi ko masu wani irin laifi ko kuma masu shisshigi.

  12. Saboda haka, ka tuna fa, abin da ka karɓa ka kuma ji; ka yi biyayya da shi, ka kuma tuba. Amma in ba ka farka ba, zan zo kamar ɓarawo, ba kuwa za ka san lokacin da zan zo maka ba.

  13. Ba su kuma tuba daga kisankansu, sihirinsu, fasikancinsu ko kuma daga sace-sacensu ba.