Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Resurrection: A doctrine of the Old Testament

6 ayoyi · 36 fannoni

Ayoyi game da A doctrine of the Old Testament

  1. Kuma bayan an hallaka fatata, duk da haka a cikin jiki zan ga Allah.

  2. domin ba za ka yashe ni a kabari ba, ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.

  3. Amma Allah zai ceci raina daga kabari; tabbatacce zai ɗauke ni zuwa wurinsa. Sela

  4. Amma matattunka za su rayu; jikunansu za su tashi. Ku da kuke zama a ƙura, ku farka ku kuma yi sowa don farin ciki. Raɓarka kamar raɓar safiya ce; duniya za tă haifi matattunta.

  5. Ɗumbun mutanen da suka yi barci cikin turɓayar duniya za su farka, waɗansu zuwa ga rai madawwami, waɗansu zuwa ga madawwamiyar kunya da kuma madawwamin ƙasƙanci.

  6. “Zan fanshe su daga ikon kabari; zan cece su daga mutuwa. Ina annobanki, ya mutuwa? Ina hallakarka, ya kabari? “Ba zan ji tausayi ba,