Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Serpents: Of the devil

4 ayoyi · 26 fannoni

Ayoyi game da Of the devil

  1. To, maciji dai ya fi kowane a cikin namun jejin da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa macen, “Tabbatacce ne Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga kowane itace a lambu’?”

  2. Sai dai ina tsoro kada yă zama, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa’u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Kiristi.

  3. Aka jefar da ƙaton jan macijin ƙasa, tsohon maciji nan da ake kira Iblis, ko Shaiɗan, wanda ya ɓad da dukan duniya. Aka jefar da shi ƙasa, tare da mala’ikunsa a duniya.

  4. Ya kama macijin, wannan tsohon maciji, wanda yake shi ne Iblis, ko kuwa Shaiɗan, aka kuma ɗaura shi har shekara dubu.