Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Self-Crimination

27 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai Ubangiji ya ce wa Musa,

  2. “Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘In matar wani ta kauce, ta kuma yi rashin aminci gare shi

  3. ta wurin kwana da wani dabam, wannan kuwa ya kasance a ɓoye ga mijinta, rashin tsarkinta kuwa bai tonu ba (da yake babu shaida, ba a kuma kama ta tana yi ba),

  4. in kuma kishi ya sha kan mijinta kuma tana da ƙazanta, ko kuwa idan yana kishi yana kuma zatonta ko ma ba ta da ƙazanta

  5. mijin zai kai matansa a gaban firist, yă kuma kawo hadayar abubuwan da ake bukata; abubuwa kamar, garin sha’ir garwa ɗaya, amma kada yă zuba mai a kan garin sha’ir, kada kuma yă sa turaren wuta a kansa, domin hadaya ce ta miji mai tuhumar matarsa da aka kawo domin gaskiya tă fito fili.

  6. “ ‘Firist zai kawo ta, yă sa tă tsaya a gaban Ubangiji.

  7. Sa’an nan zai ɗebi ruwa mai tsarki a tulun laka, yă zuba ƙurar da ya ɗebo daga daɓen tabanakul a cikin ruwan.

  8. Bayan da firist ya sa matan ta tsaya a gaban Ubangiji, sai yă kunce gashin kanta, yă kuma sa hadaya ta gari don tunawa a hannuwanta, hadayar gari ce ta kishi, yayinda shi kansa zai riƙe ruwa mai ɗaci, mai jawo la’ana.

  9. Sa’an nan firist zai sa tă yi rantsuwa, yă kuma ce mata, “In ba wani mutumin da ya kwana da ke kuma ba ki kauce kin ƙazantar da kanki yayinda kike auren mijinki ba, kada wannan ruwa mai ɗaci, mai jawo la’ana, yă cuce ki.

  10. Amma in kin kauce yayinda kike auren mijinki, kika kuma ƙazantar da kanki ta wurin kwana da wani dabam da ba mijinki ba,”

  11. (a nan firist zai sa macen a ƙarƙashin la’anar rantsuwa cewa) “bari Ubangiji yă sa mutanenki su la’ance ki, su kuma yi Allah wadai da ke, sa’ad da Ubangiji ya sa cinyarki ta shanye, cikinki kuma ya kumbura.

  12. Bari wannan ruwa mai jawo la’ana, yă shiga jikinki saboda cikinki yă kumbura, cinyarki kuma yă shanye.” “ ‘Sai macen tă ce, “Amin. Bari yă zama haka.”

  13. “ ‘Firist zai rubuta waɗannan la’anoni a littafi, sa’an nan yă wanke su cikin ruwa mai ɗaci.

  14. Sai yă sa macen tă sha ruwa mai ɗaci, mai jawo la’ana, wannan ruwa kuwa zai shiga cikinta yă kawo mata wahala mai zafi.

  15. Firist zai karɓi hadaya ta gari don kishi daga hannuwanta, yă kaɗa shi a gaban Ubangiji sa’an nan yă kawo a bagade.

  16. Sa’an nan firist zai ɗiba hatsi na hadaya cike da hannunsa don hadayar tunawa, yă kuma ƙone a bagade; bayan haka sai yă sa macen tă sha ruwan.

  17. In ta ƙazantar da kanta ta kuma ci amanar mijinta, to, yayinda aka sa tă sha ruwa mai jawo la’ana, ruwan zai shiga cikinta, yă jawo mata wahala mai zafi; cikinta zai kumbura, cinyarta kuma yă shanye, tă kuwa zama la’ananniya a cikin mutanenta.

  18. Sai Yoshuwa ya ce wa Akan, “Ɗana, sai ka ba Ubangiji, Allah na Isra’ila ɗaukaka, ka yi masa yabo. Ka gaya mini abin da ka yi; kada ka ɓoye mini.”

  19. Akan kuwa ya amsa ya ce, “Gaskiya ne! Na yi wa Ubangiji, Allah na Isra’ila zunubi. Ga abin da na yi.

  20. A cikin ganimar, na ga doguwar riga mai kyau irin ta Babilon, da shekel ɗari biyu na azurfa, da kuma sandan zinariya mai nauyin shekel hamsin, sai raina ya so su, na kuwa kwashe su. Na tona rami a cikin ƙasa a tentina; na ɓoye.”

  21. Sai Yoshuwa ya aiki ’yan aika suka tafi da gudu zuwa tenti ɗin, haka kuwa suka same su a ɓoye a tentinsa, da azurfa a ƙarƙashi.

  22. Suka kwashe kayan daga tenti ɗin suka kawo wa Yoshuwa da sauran Isra’ilawa, suka baza su a gaban Ubangiji.

  23. Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka ɗauki Akan ɗan Zera, da azurfar, doguwar rigar, sandan zinariya, ’ya’yansa maza da mata, shanunsa, jakuna da tumaki, tentinsa da duk abin da yake da shi, suka kai su Kwarin Akor.

  24. Yoshuwa ya ce, “Me ya sa ka jawo mana wahala haka? Ubangiji zai kawo maka wahala kai ma a yau.” Sai dukan Isra’ilawa suka jajjefe shi, bayan da suka gama jifarsa sai suka ƙone sauran.

  25. “Sa’ad da mutum ya yi abin da ba daidai ba ga maƙwabcinsa, an kuma bukace shi yă yi rantsuwa, sai ya zo ya rantse a gaban bagade a cikin haikalin nan,