Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prosperity

31 ayoyi · 8 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ina roƙonka ka karɓi kyautar da aka kawo maka, gama Allah ya yi mini alheri kuma ina da kome da nake bukata.” Ganin yadda Yaƙub ya nace, sai Isuwa ya karɓa.

  2. Amma bakansa yana nan daram hannuwansa masu ƙarfi ba sa jijjiguwa saboda hannun Maɗaukaki na Yaƙub, saboda Makiyayi, Dutsen Isra’ila,

  3. saboda Allah na mahaifinka, wanda ya taimake ka, saboda Maɗaukaki, wanda yake albarkace ka da albarkar sama da take bisa albarkun zurfafa da suke ƙarƙashin ƙasa albarkun mama da kuma mahaifa.

  4. Albarkun mahaifi suna da girma fiye da albarkun daɗaɗɗun duwatsu fiye da yalwar madawwaman tuddai. Bari dukan waɗannan su zauna a kan Yusuf, a goshin ɗan sarki a cikin ’yan’uwansa.

  5. Sa’ad da kuka ci, kuka ƙoshi, sai ku yabi Ubangiji Allahnku saboda ƙasa mai kyau da ya ba ku.

  6. Ku yi hankali cewa ba ku manta da Ubangiji Allahnku, har ku kāsa kiyaye umarnansa, dokokinsa da ƙa’idodinsa da nake ba ku a wannan rana ba.

  7. To, sa’ad da kuka ci, kuka ƙoshi, sa’ad da kuka gina gidaje masu kyau, kuka zauna,

  8. sa’ad da kuma garkunanku na shanu da na tumaki suka ƙaru, azurfanku da zinariyarku kuma suka ƙaru, sa’an nan dukan abin da kuke da shi ya haɓaka,

  9. to, sai ku lura, kada ku ɗaukaka kanku, har ku manta da Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta kuma.

  10. Ya bishe ku cikin hamada mai fāɗi, mai bantsoro, wannan busasshiyar ƙasa wadda ba ta da ruwa, ga macizai masu dafi da kuma kunamai. Ya ba ku ruwa daga dutsen ƙanƙara.

  11. Ya ba ku Manna don ku ci a cikin hamada, wani abin da kakanninku ba su taɓa sani ba, don yă ƙasƙantar yă kuma gwada ku, saboda yă yi muku alheri daga baya.

  12. Wataƙila ku ce wa kanku, “Ikona da ƙarfin hannuwana ne suka ba ni da wannan arziki.”

  13. Amma ku tuna da Ubangiji Allahnku, gama shi ne wanda yake ba ku azanci na yin arziki, ta haka kuwa ya tabbatar da alkawarinsa, wanda ya rantse wa kakanninku, kamar yadda yake a yau.

  14. Sa’ad da na kawo su cikin ƙasa mai zub da madara da zuma, ƙasar da na yi alkawari da rantsuwa ga kakanninsu, sa’ad da kuma suka ci suka ƙoshi, suka kuma yi ƙiba, za su juya ga waɗansu alloli su bauta musu, su ƙi ni, su kuma karya alkawarina.

  15. Yeshurun ya yi ƙiba, ya yi kauri; cike da abinci, ya zama da nauyi, ya kuma zama sumul. Ya yashe Allahn da ya yi shi, ya ƙi Dutse Cetonsa.

  16. Bayan mulkin Rehobowam ya kahu kamar sarki ya kuma yi ƙarfi, shi da dukan Isra’ila suka yi biris da dokar Ubangiji.

  17. Amma bayan Uzziya ya zama mai iko, sai ɗaga kai ya kai shi ga fāɗuwa. Bai yi aminci ga Ubangiji Allahnsa ba, ya kuma shiga haikalin Ubangiji don yă ƙone turare a bagaden turare.

  18. Amma zuciyar Hezekiya ta yi girman kai, bai kuwa yi amfani da alherin da aka nuna masa ba, saboda haka fushin Ubangiji ya sauko a kansa da kuma a kan Yahuda da Urushalima.

  19. Mutanen da ba su da damuwa suna jin daɗin ganin waɗanda suke dab da fāɗuwa.

  20. In ka komo ga Maɗaukaki, za ka warke. In ka kawar da mugunta daga cikin gidanka.

  21. Ka jefar da zinariyarka a ƙasa, ka jefar da zinariyar Ofir da ka fi so a cikin duwatsu,

  22. sa’an nan ne Maɗaukaki zai zama zinariyarka, zai zama azurfa mafi kyau a wurinka.

  23. Ba shakka a lokacin ne za ka sami farin ciki daga wurin Maɗaukaki, ku kuma ɗaga idanunku ga Allah

  24. Za ka yi addu’a zuwa gare shi, zai kuwa ji ka, kuma za ka cika alkawuranka.

  25. Waƙar haurawa. Ta Solomon. In ba Ubangiji ne ya gina gida ba, masu gininta suna wahala a banza ne. In ba Ubangiji ne yake tsaron birni ba, masu tsaro suna yin tsaro a banza.