Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prosperity: Promised to the righteous
Ayoyi game da Promised to the righteous
In ka komo ga Maɗaukaki, za ka warke. In ka kawar da mugunta daga cikin gidanka.
Ka jefar da zinariyarka a ƙasa, ka jefar da zinariyar Ofir da ka fi so a cikin duwatsu,
sa’an nan ne Maɗaukaki zai zama zinariyarka, zai zama azurfa mafi kyau a wurinka.
Ba shakka a lokacin ne za ka sami farin ciki daga wurin Maɗaukaki, ku kuma ɗaga idanunku ga Allah
Za ka yi addu’a zuwa gare shi, zai kuwa ji ka, kuma za ka cika alkawuranka.