Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Pillar: Broken and carried to Babylon

4 ayoyi · 8 fannoni

Ayoyi game da Broken and carried to Babylon

  1. Babiloniyawan kuma suka sassare ginshiƙan tagulla, da wuraren zama da za a iya matsar da su, da ƙaton kwano mai suna Teku na tagulla da yake a haikalin Ubangiji, suka kwashe tagullan zuwa Babilon.

  2. Babiloniyawa kuwa suka farfasa ginshiƙan tagulla, da dakalai, da babbar kwatarniya, waɗanda suke a haikalin Ubangiji. Suka kwashe tagulla duka suka kai Babilon.

  3. Tagullar da sarki Solomon ya yi wa haikalin Ubangiji da ita, wato, ginshiƙai biyu, da ƙaton kwano mai suna Teku na tagulla, da bijimai goma sha biyu, waɗanda suke ɗauke da kwatarniya, da dakalai, ta fi ƙarfin a auna.

  4. Tsawon kowane ginshiƙi kamu goma sha takwas ne, kewayensa kuwa kamu goma sha biyu ne, kaurinsa kuma huɗu ne. Kowannensu yana da rami a ciki.