Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Phinehas

38 ayoyi · 7 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai dai yă zama shaida tsakaninmu da ku, da kuma waɗanda za su zo a baya, cewa za mu yi wa Ubangiji sujada a wurinsa mai tsarki, za mu miƙa hadayunmu na ƙonawa, hadayu na zumunta. Sa’an nan, nan gaba ’ya’yanku ba za su ce wa ’ya’yanmu, ‘Ba ku da rabo a cikin Ubangiji ba.’

  2. “Muka kuma ce, ‘In har suka ce mana, ko ’ya’yanmu haka, sai mu amsa mu ce ku dubi bagaden da yake daidai da na Ubangiji wanda iyayenmu suka gina, ba don ƙona hadayu da kuma yin sadaka ba, sai dai don yă zama shaida tsakaninmu da ku.’

  3. “Allah ya sawwaƙa mana mu tayar wa Ubangiji mu bar binsa, har mu gina bagade don miƙa hadayu na ƙonawa, da na gari, da na sadaka, ban da bagaden Ubangiji Allahnmu wanda yake tsaye a gaban tabanakul.”

  4. Da Finehas firist, da shugabannin mutanen, shugabannin iyalan Isra’ila, suka ji abin da mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse suka ce, sai suka ji daɗi.

  5. Sai Finehas ɗan Eleyazar, firist, ya ce wa mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse, “Yau mun san Ubangiji yana tare da mu, domin ba ku yi wa Ubangiji rashin aminci cikin wannan abu ba. Yanzu kun kuɓutar da Isra’ilawa daga hannun Ubangiji.”

  6. Sai Finehas ɗan Eleyazar, firist, da shugabannin suka koma Kan’ana daga saduwa da mutanen Ruben da mutanen Gad a Gileyad, suka kai wa Isra’ilawa rahoto.

  7. Eleyazar ɗan Haruna, ya mutu aka binne shi a Gibeya, wurin da aka ba ɗansa Finehas a ƙasar kan tudu ta Efraim.

  8. Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, kuwa yana hidima a gabansa.) Suka ce, “Mu sāke haura mu yi yaƙi da mutanen Benyamin ’yan’uwanmu, ko a’a?” Ubangiji ya ce, “Ku je, gama gobe zan ba da su a hannuwanku.”

  9. Eleyazar shi ne mahaifin Finehas, Finehas mahaifin Abishuwa,

  10. Waɗannan su ne zuriyar Haruna, Eleyazar, Finehas, Abishuwa,

  11. Shallum ɗan Kore, ɗan Ebiyasaf, ɗan Kora, da ’yan’uwansa matsaran ƙofofi daga iyalin (mutanen Kohat) su suke da hakkin tsaron madogaran ƙofar Tenti kamar dai yadda kakanninsu suka kasance da hakkin tsaron mashigin mazaunin Ubangiji.

  12. A dā Finehas ɗan Eleyazar ne yake lura da matsaran, kuma Ubangiji ya kasance tare da shi.

  13. Amma Finehas ya miƙe tsaye ya ɗauki mataki, sai annobar ta daina.