Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Persia: The princes advisory in matters of administration

7 ayoyi · 9 fannoni

Ayoyi game da The princes advisory in matters of administration

  1. Ya gamshi Dariyus ya naɗa muƙaddasai 120 su yi shugabanci a duk fāɗin masarautar,

  2. ya naɗa mutum uku a bisa waɗannan muƙaddasan, Daniyel yana ɗaya daga cikin mutum ukun nan. Sai aka sa muƙaddasan nan a ƙarƙashin waɗannan uku ɗin domin kada sarki ya yi hasarar kome.

  3. To, Daniyel dai ya yi ficce a cikin shugabannin nan uku har da muƙaddasan ma, saboda waɗansu halaye nagari da yake da su, wanda ya sa sarki ya yi shiri ya ɗora shi a kan dukan mulkinsa.

  4. A kan haka, shugabannin nan uku da muƙaddasan nan suka yi ƙoƙari su sami wani laifi a kan Daniyel a yadda yake tafiyar da aikin shugabancinsa, amma ba su samu ba. Ba su same shi da wani laifin cin hanci ba, domin shi amintacce ne kuma babu wani aibi a kansa ko rashin kula.

  5. A ƙarshe waɗannan mutane suka ce; “Ba za mu taɓa samun wani laifin da za mu kama Daniyel da shi ba, sai dai ko abin ya shafi dokar Allahnsa.”

  6. Saboda haka shugabannin nan suka haɗu da muƙaddasan nan suka tafi wurin sarki a ƙungiyance suka ce, “Ya Sarki Dariyus, ranka yă daɗe!

  7. Shugabannin masarauta, da masu mulki, da muƙaddasai, da mashawarta da gwamnoni duk sun amince cewa sarki yă kafa doka yă kuma yi umarni cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda ya yi addu’a ga wani allah ko mutum, in ba a gare ka ba, ya sarki, jefa shi cikin kogon zakoki.