Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Persia: Municipal governments in, provided with dual governors
Ayoyi game da Municipal governments in, provided with dual governors
Refahiya ɗan Hur, mai mulkin rabin yankin Urushalima, ya yi gyare-gyaren sashe na biye.
Shallum ɗan Hallohesh, mai mulkin ɗayan rabin yankin Urushalima ya yi gyare-gyaren sashe na biye tare da taimakon ’ya’yansa mata.
Gaba da shi, Nehemiya ɗan Azbuk, mai mulkin rabin yankin Bet-Zur ne ya yi gyare-gyaren har zuwa kusa da kaburburan Dawuda, har zuwa haƙaƙƙen tafki da kuma Gidan Jarumawa.
Biye da shi, Lawiyawa a ƙarƙashin Rehum ɗan Bani ne suka yi gyare-gyaren. Kusa da su, Hashabiya mai mulkin rabin yankin Keyila ne ya yi gyare-gyaren don yankinsa.
Biye da shi, ’yan’uwansu Lawiyawa ne a ƙarƙashin Binnuyi ɗan Henadad, mai mulkin ɗayan rabin yankin Keyila suka yi gyare-gyaren.