Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Penitent

131 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Za ka yi addu’a zuwa gare shi, zai kuwa ji ka, kuma za ka cika alkawuranka.

  2. Abin da ka zaɓa za ka yi za ka yi nasara a ciki, haske kuma zai haskaka hanyarka.

  3. Sa’ad da aka ƙasƙantar da mutane ka kuma ce, ‘A ɗaga su!’ Sa’an nan zai ceci masu tawali’u.

  4. Zai yi gardama da ni da ikonsa mai girma? Babu, ba zai zarge ni da laifi ba.

  5. Ya yi addu’a ga Allah ya kuwa samu alheri a wurinsa, yana ganin fuskar Allah yana kuma yin sowa don murna; Allah ya mayar da shi ya zama mai adalci.

  6. Sa’an nan sai ya zo wurin, wurin mutane ya ce, ‘Na yi zunubi, na kauce wa abin da yake daidai, amma ban samu abin da ya kamata in samu ba.

  7. Ya fanshi raina daga fāɗawa cikin rami, kuma zan rayu in ji daɗin hasken.’

  8. Ku tafi daga gare ni, dukanku masu aikata mugunta, gama Ubangiji ya ji kukata.

  9. Ubangiji ya ji kukata saboda jinƙansa; Ubangiji ya karɓi addu’ata.

  10. Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai, gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba.

  11. Matalauta za su ci su ƙoshi; su da suke neman Ubangiji za su yabe shi, bari zukatanku su rayu har abada!

  12. Wa zai iya hawan tudun Ubangiji? Wa zai iya tsaya a wurinsa mai tsarki?

  13. Sai wanda yake da hannu mai tsabta da kuma tsabtar zuciya, wanda ba ya ba da ransa ga bautar gunki ko ya rantse bisa abin da yake ƙarya.

  14. Zai sami albarka daga Ubangiji da fiffitawa daga Allah Mai cetonsa.

  15. Irin tsaran waɗanda suke nemansa ke nan, waɗanda suke neman fuskarka, ya Allah na Yaƙub. Sela

  16. Sa’an nan na furta zunubina a gare ka ban kuwa ɓoye laifina ba. Na ce, “Zan furta laifofina ga Ubangiji.” Ka kuwa gafarta laifin zunubina. Sela

  17. Saboda haka bari duk mai tsoron Allah yă yi addu’a gare ka yayinda kake samuwa; tabbatacce sa’ad da manyan ruwaye suka taso, ba za su kai wurinsa ba.

  18. Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.

  19. Hadayun Allah su ne karyayyen ruhu; karyayyiya da kuma zuciya mai tuba, Ya Allah, ba za ka ƙi ba.

  20. Amma bari dukan masu nemanka su yi farin ciki su kuma yi murna a cikinka; bari waɗanda suke ƙaunar cetonka kullum su ce, “Bari Allah yă sami ɗaukaka!”

  21. Ka ƙosar da mu da safe da ƙaunarka marar ƙarewa, don mu rera don yabo, mu kuma yi murna dukan kwanakinmu.

  22. Faranta mana zuciya kamar yawan kwanakin da muka sha azaba, kamar yawan shekarun da muka ga wahala.

  23. Ubangiji yana kusa da kowa da ya kira gare shi, ga duk wanda ya kira gare shi cikin gaskiya.

  24. Yakan cika sha’awar waɗanda suke tsoronsa; yakan ji kukansu yă kuma cece su.

  25. Ya warkar da masu raunanar zuciya ya ɗaɗɗaura miyakunsu.