Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Medicine

11 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Zuciya mai farin ciki magani ne mai kyau, amma bakin rai kan busar da ƙasusuwa.

  2. Daga tafin ƙafarku zuwa saman kanku ba lafiya, sai miyaku da ƙujewa da manyan gyambuna, ba a tsabtacce su ba ko a daure ko shafa musu magani.

  3. Ishaya ya riga ya ce, “Ku shirya curin da aka yi da ’ya’yan ɓaure ku kuma shafa a marurun, zai kuwa warke.”

  4. Ba magani ne a Gileyad? Ba likita ne a can? To, me ya sa ba warkarwa wa raunin mutanena?

  5. Babu wanda zai yi roƙo saboda damuwarku, ba magani domin mikinku babu warkarwa dominku.

  6. “Ki haura Gileyad ki samo magani, Ya Budurwa ’Yar Masar. Amma kin riɓanya magani a banza; ba magani dominki.

  7. Farat ɗaya Babilon za tă fāɗi ta farfashe. Ku yi kuka dominta! Ku samo mata magani saboda azabarta; wataƙila za a iya warkar da ita.

  8. “ ‘Da mun warkar da Babilon, amma ba za tă warke ba; mu ƙyale ta kowane yă koma garinsu, gama hukuncinta ya kai sammai, ya yi tsawo kamar gizagizai.’

  9. ’Ya’yan itatuwa na kowane iri za su yi girma a kowane gefen kogin. Ganyayensu ba su bushe ba, ba kuwa za su fasa yin ’ya’ya ba. Kowane wata za su ba da ’ya’ya domin ruwa daga wuri mai tsarki yana malalo musu. ’Ya’yansu za su zama abinci, ganyayensu kuma za su zama magani.”

  10. Ya je wurinsa, ya daddaure masa raunukansa, sa’an nan ya zuba mai, da ruwan inabi. Ya ɗauki mutumin ya sa a kan jakinsa, ya kai shi wani masauƙi, ya yi jinyarsa.

  11. yana bin tsakiyar babban titi na birnin. A kowane gefen kogin akwai itacen rai mai ba da ’ya’ya goma sha biyu, yana ba da ’ya’yansa kowane wata. Ganyayen itacen kuwa saboda warkar da al’ummai ne.