Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Intercession

72 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’an nan suka ce wa Irmiya, “Ubangiji ya zama shaida na gaskiya da kuma aminci a kanmu in ba mu yi bisa da duk abin da Ubangiji Allahnka ya aike ka ka faɗa mana ba.

  2. Ko ya gamshe mu ko bai gamshe mu ba, za mu yi biyayya da Ubangiji Allahnmu, ga wanda muke aikan ka, saboda ya zama mana da amfani, gama za mu yi biyayya da Ubangiji Allahnmu.”

  3. Da Yesu ya shiga Kafarnahum, sai wani jarumi ya zo wurinsa, yana neman taimako.

  4. Ya ce, “Ubangiji, bawana yana kwance a gida shanyayye, yana kuma shan azaba ƙwarai.”

  5. Yesu ya ce masa, “Zan je in warkar da shi.”

  6. Jarumin ya amsa, “Ubangiji, ban cancanci in sa ka zo gidana ba, ka dai yi magana kawai, bawana zai warke.

  7. Gama ni kaina mutum ne a ƙarƙashin iko, da kuma sojoji a ƙarƙashina. Nakan ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai yă tafi; wancan kuma, ‘Zo nan,’ sai yă zo. Nakan ce wa bawana, ‘Yi wannan,’ sai kuwa yă yi.”

  8. Da Yesu ya ji wannan, sai ya yi mamaki ya kuma ce wa waɗanda suke binsa, “Gaskiya nake gaya muku, ban taɓa samun wani a Isra’ila da bangaskiya mai girma haka ba.

  9. Ina kuma gaya muku da yawa za su zo daga gabas da kuma yamma, su ɗauki wuraren zamansu a biki tare da Ibrahim, Ishaku, da Yaƙub a cikin mulkin sama.

  10. Amma za a jefar da ’ya’yan mulki waje, zuwa cikin baƙin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.”

  11. Sa’an nan Yesu ya ce wa jarumin, “Je ka! Za a yi bisa ga bangaskiyarka.” A daidai wannan lokaci bawansa kuwa ya warke.

  12. Suka gama yankin da gudu, suna ɗaukan marasa lafiya a kan tabarmai zuwa duk inda suka ji yake.

  13. Duk inda ya shiga, cikin ƙauyuka, birane ko karkara, sai su kwantar da marasa lafiya a bakin kasuwa. Suka roƙe shi yă bari su taɓa gefen rigarsa kawai, kuma duk waɗanda suka taɓa shi kuwa, suka warke.

  14. Da farko dai, ina gargaɗe ku cewa a yi roƙe-roƙe, ana addu’o’i, ana yin addu’a a madadin waɗansu da kuma a yi godiya saboda kowane mutum

  15. da sarakuna da dukan masu mulki, domin mu zauna lafiya, rai kuma kwance, muna bin Allah sosai a cikin natsuwa.

  16. Akwai waninku da yake ciwo? Ya kamata yă kira dattawan ikkilisiya su yi masa addu’a, su kuma shafa masa mai cikin sunan Ubangiji.

  17. Addu’ar da aka yi cikin bangaskiya, za tă warkar da marar lafiya, Ubangiji zai tashe shi. In ya yi zunubi kuwa za a gafarta masa.

  18. Saboda haka, ku furta wa juna zunubanku, ku yi addu’a saboda juna, domin ku sami warkarwa. Addu’ar mai adalci tana da iko da kuma amfani.

  19. Iliya mutum ne kamar mu. Ya yi addu’a da gaske don kada a yi ruwan sama, ba a kuma yi ruwan sama a ƙasar ba har shekaru uku da rabi.

  20. Ya sāke yin addu’a, sai sammai suka ba da ruwan sama, ƙasa kuma ta ba da amfaninta.

  21. ’Yan’uwana, in waninku ya kauce daga gaskiya, wani kuma ya komo da shi,

  22. sai yă tuna da wannan. Duk wanda ya komo da mai zunubi daga kaucewarsa, zai cece shi daga mutuwa, yă kuma rufe zunubai masu ɗumbun yawa.