- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Intercession
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
“Duk sa’ad da Haruna zai shiga Wuri Mai Tsarki, zai shiga riƙe da sunayen ’ya’yan Isra’ila a zuciyarsa a kan ƙyallen maƙalawa a ƙirji na neman nufin Allah, domin yă zama abin tunawa a gaban Ubangiji.
Ka kuma sa Urim da Tummim a ƙyallen maƙalawa a ƙirji, don su kasance a zuciyar Haruna, a duk sa’ad da zai shiga gaban Ubangiji. Haka kuwa kullum Haruna zai riƙa kai koke-koken Isra’ilawa a gaban Ubangiji.
Ubangiji ya ce wa Musa, “Na ga waɗannan mutane, mutane ne masu taurinkai.”
Yanzu ka bar ni kurum fushina yă yi ƙuna a kansu, in hallaka su. Sa’an nan in maishe ka al’umma mai girma.
Amma Musa ya nemi tagomashin Ubangiji, Allahnsa ya ce, “Ya Ubangiji don me fushinka zai yi ƙuna a kan mutanenka, waɗanda ka fisshe su daga Masar da ikon hannunka mai girma?
Don me za ka sa Masarawa su ce, ‘Ai, da mugun nufi ne ya fito da su don yă shafe su daga fuskar duniya’? Ka juya daga fushinka mai zafi, ka ji tausayi, kada ka kawo masifa a kan mutanenka.
Ka tuna da bayinka Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, waɗanda ka rantse da kanka cewa, ‘Zan mai da zuriyarka kamar taurarin sama kuma zan ba wa zuriyarka wannan ƙasa wadda na yi musu alkawari, za tă kuma zama abin gādonsu har abada.’ ”
Sai Ubangiji ya yi juyayi, bai kuwa kawo wa mutanensa bala’in da ya yi niyya ba.
“Gaya wa Haruna da ’ya’yansa, ‘Ga yadda za ku albarkaci Isra’ilawa. Za ku ce musu,
“ ‘ “Ubangiji yă albarkace ku, yă kuma kiyaye ku;
Ubangiji yă sa fuskarsa ta haskaka a kanku, yă kuma yi muku alheri;
Ubangiji yă dube ku da idon rahama, yă kuma ba ku salama.” ’
Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yaushe mutanen nan za su rena ni? Har yaushe za su ƙi gaskata da ni, duk da yawan mu’ujizan da nake yi a cikinsu?
Zan buge su duka da annoba, in hallaka su, amma zan mai da kai al’umma mai girma, da kuma ƙarfi fiye da su.”
Sai Musa ya ce wa Ubangiji, “Ai, Masarawa za su ji game da wannan! Da ikonka ka fitar da mutanen nan daga cikinsu.
Za su kuwa gaya wa mutanen wannan ƙasa. Sun riga sun ji cewa kai, ya Ubangiji, kana tare da waɗannan mutane, kuma cewa kai, ya Ubangiji, an gan ka fuska da fuska, cewa girgijenka ya tsaya bisansu, cewa kana tafiya a gabansu cikin ginshiƙin girgije da rana, da ginshiƙin wuta kuma da dare.
In ka kashe dukan mutanen nan gaba ɗaya, al’ummai da suka ji wannan labari game da kai za su ce,
‘Ubangiji ya kāsa kai waɗannan mutane a ƙasar da ya yi alkawari da rantsuwa ne, shi ya sa ya kashe su a hamada.’
“Yanzu bari Ubangiji yă nuna ikonsa, kamar dai yadda ka furta.
‘Ubangiji mai jinkiri fushi ne, mai yawan ƙauna, mai gafarta zunubi da tawaye. Duk da haka ba ya ƙyale mai laifi, babu horo. Yana horin ’ya’ya saboda zunubin iyayensu har tsara ta uku, da ta huɗu.’
Bisa ga ƙaunarka mai girma, ka gafarta zunubin mutanen nan, kamar dai yadda ka gafarta musu daga lokacin da suka bar Masar har zuwa yanzu.”
Ubangiji ya amsa ya ce, “Na gafarta musu, yadda ka roƙa.
Sai Musa ya ce wa Haruna, “Ka ɗauki farantinka ka sa turare a ciki, da wuta daga bagade, ka yi maza ka tafi wajen taron, ka yi kafara dominsu. Gama fushin Ubangiji ya riga ya sauko; an kuma fara annoba.”
Saboda haka Haruna ya yi kamar yadda Musa ya faɗa, ya ruga a guje zuwa tsakiyar taron. An riga an fara annobar a cikin mutane, amma Haruna ya miƙa turaren ya kuma yi kafara dominsu.
Ya tsaya tsakanin matattu da masu rai, annobar kuwa ta tsaya.