Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Harlot

47 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Ina da hadaya ta salama a gida; yau zan cika alkawarina.

  2. Saboda haka na fito don in sadu da kai; na neme ka na kuma same ka!

  3. Na lulluɓe gadona da lili masu launi dabam-dabam daga Masar.

  4. Na yayyafa turare a gadona da mur, aloyes da kuma kirfa.

  5. Zo, mu sha zurfin ƙauna har safe; bari mu ji wa ranmu daɗi da ƙauna!

  6. Mijina ba ya gida; ya yi tafiya mai nisa.

  7. Ya ɗauki jakarsa cike da kuɗi ba zai kuwa dawo gida ba sai tsakiyar wata.”

  8. Da kalmomin rarrashi ta sa ya kauce; ta ɗauki hankalinsa da sulɓin maganarta.

  9. Nan take, ya bi ta kamar saniyar da za a kai mayanka, kamar wawa zuwa wurin da za a ba shi horo

  10. sai da kibiya ta soki hantarsa, kamar tsuntsun da ya ruga cikin tarko, ba tare da sani zai zama sanadin ransa ba.

  11. Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; ku kasa kunne ga abin da nake faɗa.

  12. Kada ku bar zuciyarku ta juya zuwa hanyoyinta ko ku kauce zuwa hanyoyinta.

  13. Ta zama sanadin fāɗuwar yawanci; kisan da ta yi ba ta ƙidayuwa.

  14. Gidanta babbar hanya ce zuwa kabari mai yin jagora zuwa ɗakunan lahira.

  15. Wawancin mace a bayyane yake; ba ta da ɗa’a kuma ba ta da sani.

  16. Takan zauna a ƙofar gidanta, a wurin zama a wurin mafi tsayi na birni,

  17. tana kira ga masu wucewa, waɗanda suke tafiya kai tsaye a hanyarsu.

  18. “Bari dukan waɗanda suke marasa azanci su zo cikin nan!” Tana ce wa marasa hankali.

  19. “Ruwan da aka sata ya fi daɗi; abincin da aka ci a ɓoye ya fi daɗi!”

  20. Amma ba su san cewa matattu suna a can ba, cewa baƙinta suna a can cikin zurfin kabari ba.

  21. A wannan lokaci za a manta da Taya har shekaru saba’in, tsawon rayuwar sarki. Amma a ƙarshen waɗannan shekaru saba’in, zai zama wa Taya kamar yadda yake a waƙar karuwa cewa,

  22. “Ɗauki garaya, ki ratsa birni, Ya ke karuwar da aka manta da ita; kaɗa garaya da kyau, ki rera waƙoƙi masu yawa, saboda a tuna da ke.”