Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Gifts from God: Unclassified scriptures relating to both temporal and spiritual

41 ayoyi · 5 fannoni

Ayoyi game da Unclassified scriptures relating to both temporal and spiritual

Tace bisa littafi
  1. Yana sāke lokuta, yana tuɓe sarakuna yana kuma naɗa waɗansu. Yana ba da hikima ga masu hikima kuma ilimi ga masu basira.

  2. Yakan bayyana zurfafa da ɓoyayyun abubuwa; ya san abin da yake cikin dare, haske kuwa yana zaune tare da shi.

  3. Na gode maka ina yabonka, Allah na kakannina. Kai ka san hikima da iko, ka sanar da ni abin da muka tambaye ka, ka kuma sanar da mu mafarkin sarki.”

  4. “Har wa yau, za a kwatanta shi da mutumin da zai yi tafiya, wanda ya kira bayinsa ya kuma danƙa musu mallakarsa.

  5. Ga guda, ya ba shi talenti biyar na kuɗi, ga wani talenti biyu, ga wani kuma talenti ɗaya, kowa bisa ga azancinsa. Sa’an nan ya yi tafiyarsa.

  6. Mutumin da ya karɓi talenti biyar, nan da nan ya tafi ya yi kasuwanci da su har ya sami ribar talenti biyar.

  7. Haka ma, wannan mai talenti biyu, shi ma ya yi riba biyu.

  8. Amma mutumin da ya karɓi talenti ɗaya ɗin, ya tafi, ya tona rami, ya ɓoye kuɗin maigidansa.

  9. “Bayan an daɗe, sai maigidan bayin nan ya dawo, ya kuma daidaita lissafi da su.

  10. Mutumin da ya karɓi talenti biyar, ya kawo ƙarin talenti biyar. Ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talenti biyar. Ga shi, na yi ribar biyar.’

  11. “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’

  12. “Mutumin da yake da talenti biyu, shi ma ya zo ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talenti biyu; ga shi, na yi ribar biyu.’

  13. “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’

  14. “Sa’an nan mutumin da ya karɓi talenti ɗaya ya zo. Ya ce, ‘Maigida, na san cewa kai mutum ne mai wuyan sha’ani, kana girbi inda ba ka shuka ba, kana kuma tara inda ba ka yafa iri ba.

  15. Saboda haka na ji tsoro, na je na ɓoye talentinka a ƙasa. Ga abinka.’

  16. “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Kai mugun bawa, mai ƙyuya! Ashe, ka san cewa ina girbi inda ban yi shuka ba, ina kuma tarawa inda ban yafa iri ba?

  17. To, in haka ne, ai, da ka sa kuɗina a banki, don sa’ad da na dawo da na karɓi abina da riba.

  18. “ ‘Karɓi talentin daga hannunsa ku ba wanda yake da talenti goma.

  19. Gama duk mai abu za a ƙara masa, zai kuma same shi a yawalce. Duk wanda ba shi da shi kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.

  20. Ku jefar da banzan bawan nan waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’

  21. A ranan nan, ba za ku sāke tambaya ta kome ba. Gaskiya nake gaya muku, Ubana zai ba ku kome da kuka roƙa cikin sunana.

  22. Har yanzu dai ba ku roƙi kome cikin sunana ba. Ku roƙa za ku kuwa samu, farin cikinku kuwa zai zama cikakke.

  23. Kyautar Allah kuwa ba kamar sakamakon da ya bi zunubin mutum gudan nan ba ne, Hukuncin ya bi zunubin mutum gudan nan, ya kuma kawo hallaka, amma kyautar ta bi laifofin masu yawa ta kuma sa Allah ya gan mu a matsayin marasa laifi.

  24. Gama in, ta wurin laifin mutum ɗaya, mutuwa ta yi mulki ta wurin mutum ɗayan nan, ashe, waɗanda suka sami kyautar alherin Allah a yalwace da kuma kyautar adalci za su yi mulki a wannan rayuwa ta wurin mutum ɗayan nan, Yesu Kiristi.

  25. Saboda haka, kamar yadda sakamakon laifin mutum guda ya jawo hallaka ga dukan mutane, haka ma sakamakon aikin adalci guda ya sa Allah ya same mu marasa laifi, wannan kuwa kawo rai ga dukan mutane.