Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Friendship: General references

31 ayoyi · 1 fanni

Ayoyi game da General references

Tace bisa littafi
  1. In ɗan’uwanka, ko ɗanka, ko ’yarka, ko matar da kake ƙauna, ko abokinka na kusa, a ɓoye ya ruɗe ka, yana cewa, “Mu je mu yi wa waɗansu alloli sujada” (allolin da ko kai, ko kakanninka ba su sani ba,

  2. allolin mutanen kewayenku, ko na kusa, ko na nisa, daga wannan ƙarshen ƙasar zuwa wancan),

  3. kada ka yarda da shi, kada ma ka saurare shi. Kada ka ji tausayinsa. Kada ka haƙura da shi, ko ka tsare shi.

  4. Dole ka kashe shi. Dole hannunka yă zama na farko a kisansa, sa’an nan hannuwan sauran dukan mutane.

  5. “Duk wanda ya ƙi yă yi alheri ga aboki ya rabu ta tsoron Maɗaukaki.

  6. Amma ’yan’uwana sun nuna ba zan iya dogara gare su ba, kamar rafin da yakan bushe da rani,

  7. “Ya raba ni da ’yan’uwana maza; abokaina sun zama baƙi gare ni.

  8. Dangina sun tafi; abokaina na kurkusa sun manta da ni.

  9. Waɗanda sukan ziyarce ni, da masu yi mini aiki mata sun ɗauke ni baƙo.

  10. Na kira bawana, amma bai amsa ba, ko da yake na roƙe shi da bakina.

  11. Numfashina yana ɓata wa matata rai; ’yan’uwana sun ƙi ni.

  12. Har ’yan yara suna rena ni; in sun gan ni sai su fara yi mini riyar reni.

  13. Duk abokaina sun yashe ni; waɗanda nake ƙauna sun zama ba sa ƙaunata.

  14. Ni ba kome ba ne sai dai fata da ƙashi, da ƙyar na tsira.

  15. “Ku tausaya mini, abokaina, ku ji tausayina, gama hannun Allah ya sauko a kaina.

  16. Don me kuke fafarata kamar yadda Allah yake yi? Ba ku gaji da yagar fatata ba?

  17. Duk da haka sa’ad da suke ciwo, na sanya rigar makoki na ƙasƙantar da kaina da azumi. Sa’ad da aka mayar mini da addu’o’i babu amsa,

  18. nakan yi ta yawo ina makoki sai ka ce yadda nake yi wa abokina ko ɗan’uwana. Nakan sunkuyar da kaina cikin baƙin ciki sai ka ce ina kuka domin mahaifiyata.

  19. Da a ce abokin gāba ne ke zagina, da na jure da shi; da a ce maƙiyi yana tā da kansa a kaina, da na ɓoye daga gare shi.

  20. Amma kai ne, mutum kamar ni, abokina, abokina na kurkusa,

  21. wanda na taɓa jin daɗin zumunci da shi sosai yayinda muke tafiya tare a taron jama’a a gidan Allah.

  22. Kada ka yi abokantaka da mai zafin rai, kada ka haɗa kai da wanda ba shi da wuya ya yi fushi,

  23. in ba haka ba za ka koyi hanyoyinsa ka kuma sa kanka a tarko.

  24. Kada ka zama mai ɗaukar lamuni ko ka ba da jingina saboda bashi;

  25. gama in ka kāsa biya za a ƙwace gadon da kake kwanciya a kai ma.