Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Family

44 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka ya ba da umarni a yi musu baftisma cikin sunan Yesu Kiristi. Sa’an nan suka roƙi Bitrus yă zauna da su na ’yan kwanaki.

  2. Wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu’a suna rera waƙoƙi ga Allah, sauran ’yan kurkuku kuwa suna sauraronsu.

  3. Ba zato ba tsammani sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa har tushen ginin kurkukun ya jijjiga. Nan da nan sai duk ƙofofin kurkukun suka bubbuɗe, sarƙoƙin kowa kuma suka ɓaɓɓalle.

  4. Mai gadin kurkukun ya farka daga barci, sa’ad da ya ga ƙofofin kurkukun a buɗe, sai ya zāre takobinsa yana shirin kashe kansa domin ya ɗauka ’yan kurkukun sun gudu.

  5. Amma Bulus ya yi ihu ya ce, “Kada ka yi wa kanka lahani! Dukanmu muna nan!”

  6. Mai gadin kurkukun ya kira a kawo fitilu, ya ruga ciki ya fāɗi yana rawan jiki a gaban Bulus da Sila.

  7. Sai ya fito da su waje ya kuma tambaye su ya ce, “Ranku yă daɗe, me zan yi domin in sami ceto?”

  8. Suka amsa suka ce, “Ka gaskata da Ubangiji Yesu, za ka sami ceto, kai da iyalinka.”

  9. Sa’an nan suka yi masa maganar Ubangiji shi da kuma dukan sauran da suke a gidansa.

  10. A wannan sa’a na daren, mai gadin kurkukun ya ɗauke su ya wanke musu raunukansu; nan take aka yi masa baftisma da dukan iyalinsa.

  11. Sai mai gadin kurkukun ya kawo su cikin gidansa ya ba su abinci; ya kuwa cika da murna don yă gaskata da Allah, shi da dukan iyalinsa.

  12. Namiji kuwa bai kamata ya rufe kansa ba, da yake shi kamannin Allah ne, da kuma darajar Allah, amma mace dai, darajar namiji ne.

  13. Gama namiji bai fito daga mace ba, sai dai mace ce ta fito daga namiji.

  14. Ba a kuma halicci namiji don mace ba, sai dai mace don namiji.

  15. Matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, kamar ga Ubangiji ne kuke yi.

  16. Gama miji shi ne kan mace, yadda Kiristi yake kai da kuma Mai Ceton ikkilisiya, wadda take jikinsa.

  17. To, kamar yadda ikkilisiya take biyayya ga Kiristi, haka ma ya kamata mata su yi biyayya ga mazansu cikin kome.

  18. Dole yă iya tafiyar da iyalinsa da kyau, yă kuma tabbata cewa ’ya’yansa suna yin masa biyayya da ladabin da ya dace.

  19. (In mutum bai san yadda zai tafiyar da iyalinsa ba, yaya zai iya kula da ikkilisiyar Allah?)