Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Family: Government of

8 ayoyi · 3 fannoni

Ayoyi game da Government of

  1. Namiji kuwa bai kamata ya rufe kansa ba, da yake shi kamannin Allah ne, da kuma darajar Allah, amma mace dai, darajar namiji ne.

  2. Gama namiji bai fito daga mace ba, sai dai mace ce ta fito daga namiji.

  3. Ba a kuma halicci namiji don mace ba, sai dai mace don namiji.

  4. Matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, kamar ga Ubangiji ne kuke yi.

  5. Gama miji shi ne kan mace, yadda Kiristi yake kai da kuma Mai Ceton ikkilisiya, wadda take jikinsa.

  6. To, kamar yadda ikkilisiya take biyayya ga Kiristi, haka ma ya kamata mata su yi biyayya ga mazansu cikin kome.

  7. Dole yă iya tafiyar da iyalinsa da kyau, yă kuma tabbata cewa ’ya’yansa suna yin masa biyayya da ladabin da ya dace.

  8. (In mutum bai san yadda zai tafiyar da iyalinsa ba, yaya zai iya kula da ikkilisiyar Allah?)