Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Family

44 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai mutumin ya ce, “Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana nama kuma na namana. Za a ce da ita ‘mace,’ gama an ciro ta daga namiji.”

  2. Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.

  3. Ubangiji ya bayyana ga Abram ya ce, “Ga zuriyarka ne zan ba da wannan ƙasa.” Saboda haka Abram ya gina bagade a can ga Ubangiji, wanda ya bayyana gare shi.

  4. Daga can, ya ci gaba zuwa wajen tuddai a gabashin Betel ya kafa tentinsa, Betel yana yamma, Ai, kuma a gabas. A can ya gina bagade ga Ubangiji ya kuma kira bisa sunan Ubangiji.

  5. Daga Negeb, ya ci gaba da tafiyarsa a wurare dabam-dabam har ya kai tsakanin Betel da Ai, a inda dā ya kafa tentinsa na fari

  6. da kuma inda dā ya gina bagade. A can Abram ya kira bisa sunan Ubangiji.

  7. Daga yanzu duk namijin da aka haifa a cikinku za a yi masa kaciya a rana ta takwas har dukan zamananku, ko haifaffen gida ne, ko sayayye da kuɗi daga kowane baƙo wanda ba na zuriyarku ba.

  8. Ko haifaffe a gidanka ko an sayo da kuɗi, dole a yi musu kaciya. Alkawarina cikin jikinku zai kasance madawwamin alkawari.

  9. Kowane namijin da ba a yi masa kaciya a jiki ba, za a fid da shi daga cikin mutanensa; domin ya karya alkawarina.”

  10. Ku kula, ku kuma lura da kanku sosai, don kada ku manta da abubuwan da idanunku suka gani, ko kuwa ku bari su fita daga zuciyarku muddin ranku. Ku koyar da su ga ’ya’yanku, da ’ya’yan ’ya’yanku.

  11. Ku tuna da ranar da kuka tsaya a gaban Ubangiji Allahnku a Horeb, sa’ad da ya ce mini, “Ka tara mutane a gabana, don su ji maganata, su koya yin mini bangirma muddin ransu a ƙasar, su kuma iya koyar da su ga ’ya’yansu.”

  12. Ku koyar da su ga ’ya’yanku, ku yi ta haddace su, sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.

  13. Ku rubuta su a kan madogaran ƙofofin gidajenku, da a kan ƙofofinku,

  14. Amma sai ku nemi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa daga cikin dukan kabilanku, inda zai sa Sunansa, yă mai wurin mazauninsa. A wannan wuri ne za ku tafi;

  15. a can ne kuma za ku kawo hadayun ƙonawa da sadakoki, zakkarku da kyautai na musamman, da abin da kuka yi alkawari za ku bayar, da hadayunku na yardar rai, da kuma ’ya’yan farin garkunanku na shanu da na tumaki.

  16. A can, a gaban Ubangiji Allahnku, ku da iyalanku za su ci, su kuma yi farin ciki a kome da kuka sa hannunku a kai, domin Ubangiji Allahnku zai albarkace ku.

  17. sai ku kai dukan abin da na umarce ku ku kai, wato, hadayu na ƙonawa, da sadakokinku, da zakkarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na alkawarin da kuka yi wa Ubangiji a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa yă sa sunansa.

  18. A can kuma za ku yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku, ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da kuma Lawiyawa daga biranenku, waɗanda ba a ba su rabo ba, ba su kuma da gādo na kansu.

  19. A Kaisariya akwai wani mutum mai suna Korneliyus, wani jarumin Roma ne, a ƙungiyar soja da ake kira Bataliyar Italiya.

  20. Shi da dukan iyalinsa masu ibada ne masu tsoron Allah kuma; yakan ba da kyauta hannu sake ga masu bukata yana kuma addu’a ga Allah ba fasawa.

  21. Wata rana wajen ƙarfe uku na yamma ya ga wahayi. A sarari ya ga wani mala’ikan Allah, wanda ya zo wajensa ya ce, “Korneliyus!”

  22. Korneliyus kuwa ya zura masa ido a tsorace ya ce, “Mene ne, ya Ubangiji?” Mala’ikan ya ce, “Addu’o’inka da kyautanka ga matalauta sun kai har sama, hadayar tunawa ce a gaban Allah.

  23. Yanzu sai ka aiki mutane zuwa Yoffa su dawo da wani mutum mai suna Siman wanda ake kira Bitrus.

  24. Yana zama tare da Siman, mai aikin fatu, wanda gidansa ke bakin teku.”

  25. “Wani zai iya hana a yi wa waɗannan mutane baftisma da ruwa? Sun karɓi Ruhu Mai Tsarki kamar yadda muka karɓa.”