Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Drunkenness

52 ayoyi · 31 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Za su ce wa dattawan, “Wannan ɗanmu gagararre ne, mai tawaye. Ba ya mana biyayya. Mai zari ne, kuma mashayi.”

  2. Sa’an nan dukan mazan garinsa za su jajjefe shi har yă mutu. Dole ku fid da mugu daga cikinku. Dukan Isra’ila kuwa za su ji wannan su kuma ji tsoro.

  3. Idan kuma wani mutum ya ji kalmomi na wannan rantsuwa, ya kuma sa wa kansa albarka yana tunani cewa, “Ba abin da zai same ni, ko da na nace a taurinkaina.” Wannan zai jawo lalacewar dukan Isra’ila tare da kai.

  4. Ubangiji ba zai gafarce shi ba, fushinsa da kishinsa za su ƙuna a kan wannan mutum. Dukan la’anonin da aka rubuta a wannan littafi za su fāɗo a kansa, Ubangiji kuwa zai shafe sunansa daga ƙarƙashin sama.

  5. Ubangiji zai ware shi daga dukan kabilan Isra’ila don yă hukunta shi bisa ga dukan la’anonin alkawarin da aka rubuta a wannan Littafin Doka.

  6. Kada ka haɗa kai da waɗanda suke shan ruwan inabi da yawa ko masu haɗama kansu da abinci,

  7. gama bugaggu da ruwan inabi da masu yawan ci sukan zama matalauta, gama jiri yakan yi musu sutura da tsummoki.

  8. Wa yake wayyo? Wa yake baƙin ciki? Wa yake neman fada? Wa yake gunaguni? Wa yake da raunuka ba dalili? Wa yake da jan idanu?

  9. Waɗanda suke daɗe suna shan ruwan inabi, waɗanda suke neman ƙoƙon damammen ruwan inabi.

  10. Kada ka ƙyifce ido a ruwan inabi sa’ad da ya yi ja, sa’ad da yana da kyan gani a cikin ƙwarya, sa’ad da yana gangarawa sumul a maƙogwaro!

  11. A ƙarshe yana sara kamar maciji da kuma dafi kamar gamsheƙa.

  12. Idanunka za su riƙa gane-gane, zuciyarka kuma za su riƙa tunani abubuwa masu rikitarwa.

  13. Za ka zama kamar wanda yake barci a tsakiyar tekuna, kwance a sama itacen jirgin ruwa.

  14. Za ka ce “Sun buge ni, amma ban ji ciwo ba! Sun daddoke ni, amma ba na jin zafinsa! Yaushe zan farka don in ƙara shan wani?”

  15. “Ba na sarakuna ba ne, ya Lemuwel, ba na sarakuna ba ne su sha ruwan inabi, ba na masu mulki ba ne su yi marmarin barasa,

  16. don kada su sha su manta da abin da doka ta umarta, su hana wa waɗanda aka danne hakkinsu.

  17. A ba da barasa ga waɗanda suke cikin halin ƙaƙa naka yi, ruwan inabi ga waɗanda suke cikin wahala;

  18. bari su sha su manta da talaucinsu kada kuma su ƙara tunawa da ɓacin ransu.

  19. Kaiton waɗanda suke tashi da sassafe don su nufi wurin shaye-shaye, waɗanda suke raba dare har sai sun bugu da ruwan inabi.

  20. Suna kaɗa garaya, da molaye a bukukkuwansu, ganguna da busa da ruwan inabi, amma ba su kula da ayyukan Ubangiji ba, ba sa biyayya ga aikin hannuwansa.

  21. Kaito ga wannan rawani, girman kai na mashayan Efraim, ga fure mai yanƙwanewa, darajar kyansa, da aka sa a kan kwari mai ba da amfani, ga birnin nan, wadda take girman kan waɗanda aka ƙasƙantar da ruwan inabinsu!

  22. Duba, Ubangiji yana da wanda yake da iko da kuma ƙarfi. Kamar dutsen ƙanƙara da kuma iska mai ɓarna, kamar kwararowar ruwa da rigyawa mai kirmewa, zai jefa shi har ƙasa da ƙarfi.

  23. Za a tattaka wannan rawani, girman kai na mashayan Efraim da ƙafa.

  24. Da waɗannan kuma masu tangaɗi saboda sun sha ruwan inabi suke jiri don sun sha barasa Firistoci da annabawa suna tangaɗi saboda sun sha barasa sun kuma yi tatur da ruwan inabi; suna jiri saboda sun sha barasa, suna tangaɗi sa’ad da suke ganin wahayi, suna tuntuɓe sa’ad da suke ba da shawara.

  25. Duk amai ya rufe teburori kuma babu wani wurin da ba a ɓata ba.