Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Curse

47 ayoyi · 9 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku, ku bi umarnansa da ƙa’idodin da nake ba ku a yau.”

  2. A wannan rana Musa ya umarce mutane,

  3. Sa’ad da kuka haye Urdun, sai waɗannan kabilai su tsaya a bisa Dutsen Gerizim su sa wa jama’a albarka, wato, kabilar Simeyon, Lawi, Yahuda, Issakar, Yusuf da Benyamin.

  4. Waɗannan kabilai kuma za su tsaya a bisa Dutsen Ebal su furta la’ana, wato, kabilar Ruben, Gad, Asher, Zebulun, Dan da Naftali.

  5. Lawiyawa za su karanta wa dukan mutanen Isra’ila da babbar murya su ce,

  6. “La’ananne ne mutumin da ya sassaƙa siffa, ko ya yi zubin gunki, abar ƙyama ce ga Ubangiji, aikin hannu mai sana’a da aka kafa a ɓoye.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”

  7. “La’ananne ne mutumin da ya ƙasƙantar da mahaifinsa ko mahaifiyarsa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”

  8. “La’ananne ne mutumin da ya gusar da dutsen da aka kafa don nuna shaidar iyaka.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”

  9. “La’ananne ne mutumin da ya karkatar da makaho daga hanya.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”

  10. “La’ananne ne mutumin da ya yi rashin adalci ga baƙo, maraya ko gwauruwa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”

  11. “La’ananne ne mutumin da ya kwana da matar mahaifinsa, gama ya ƙasƙantar da gadon mahaifinsa ke nan.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”

  12. “La’ananne ne mutumin da ya yi jima’i da dabba.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”

  13. “La’ananne ne mutumin da ya kwana da ’yar’uwarsa, ’yar mahaifinsa ko ’yar mahaifiyarsa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”

  14. “La’ananne ne mutumin da ya kwana da mahaifiyar matarsa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”

  15. “La’ananne ne mutumin da ya kashe maƙwabcinsa a ɓoye.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”

  16. “La’ananne ne mutumin da ya karɓi cin hanci don yă kashe marar laifi.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”

  17. “La’ananne ne mutumin da bai yi na’am da kalmomin wannan doka ta wurin aikata su ba.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”

  18. Yoshuwa kuwa ya yi wa Ubangiji, Allah na Isra’ila bagade a Dutsen Ebal,

  19. kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya umarci Isra’ilawa. Ya gina bisa ga abin da yake a rubuce a cikin Littafin Dokoki na Musa, bagade na duwatsun da ba a sassaƙa su ba, waɗanda ba wani ƙarfen da ya taɓa su. Suka miƙa wa Ubangiji hadayu na ƙonawa da hadayu na salama a kai.

  20. A can, a gaban Isra’ilawa, Yoshuwa ya rubuta dokokin Musa a kan duwatsun.

  21. Sai Isra’ilawa duka, da baƙi, da haifaffun gida, da dattawansu, da shugabanninsu, da alƙalansu, suka tsaya a gefe-gefen akwatin alkawarin Ubangiji, suna fuskantar waɗanda suke ɗauke da shi, wato, firistoci waɗanda su ne Lawiyawa. Rabin mutanen suka tsaya a gaban Dutsen Gerizim, rabinsu kuma suka tsaya a gaban Dutsen Ebal, kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya riga ya umarta, cewa su sa wa mutanen Isra’ilawa albarka.

  22. Bayan haka, Yoshuwa ya karanta duk abin da yake a cikin Dokoki, albarku da la’anoni, kamar yadda suke a rubuce a cikin Littafin Dokoki.