Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Compared To Saints: Lebanon
Ayoyi game da Lebanon
Zan zama kamar raɓa ga Isra’ila zai yi fure kamar lili. Kamar al’ul na Lebanon zai sa saiwarsa zuwa ƙasa;
tohonsa za su yi girma. Darajarsa za tă zama kamar itacen zaitun, ƙanshinsa kamar al’ul na Lebanon.
Mutane za su sāke zauna a inuwarsa. Zai haɓaka kamar ƙwayar hatsi. Zai yi fure kamar kuringa, zai zama sananne kamar ruwan inabi daga Lebanon.