Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Babylon: Captivity of the Jews by

13 ayoyi · 73 fannoni

Ayoyi game da Captivity of the Jews by

  1. Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan maishe ka abin razana ga kanka da kuma ga dukan abokanka; da idanunka za ka gan takobin abokan gāba yana kashe su. Zan miƙa Yahuda duka ga sarkin Babilon, wanda zai kwashe su zuwa Babilon ya kuma kashe su da takobi.

  2. Zan ba wa abokan gābansu dukan dukiyar wannan birni dukan amfaninsa, dukan abubuwa masu daraja na sarakunan Yahuda. Za su kwashe su ganima su kai su Babilon.

  3. Kai kuma Fashhur, da dukan waɗanda suke a gidanka za ku tafi zaman bauta a Babilon. A can za ku mutu a kuma binne ku, da kai da dukan abokanka waɗanda ka yi musu annabce-annabcen ƙarya.’ ”

  4. “Ka haura zuwa Lebanon ka yi kuka, bari a ji muryarka a Bashan, yi kuka daga Abarim, gama an murƙushe dukan abokanka.

  5. Na ja maka kunne sa’ad da kake zama lafiya, amma sai ka ce, ‘Ba zan saurara ba!’ Wannan halinka ne tun kana matashi; ba ka yi mini biyayya ba.

  6. Iska za tă koro dukan makiyayanka abokanka kuma za su tafi zaman bauta. Sa’an nan za ka sha kunya a kuma walaƙanta ka saboda dukan muguntarka.

  7. Kai da kake zama a ‘Lebanon,’ kai da kake sheƙa a gine-ginen al’ul za ka yi nishi sa’ad da zafi ya auka maka, zafi kamar na mace mai naƙuda!

  8. “Muddin ina raye,” in ji Ubangiji, “ko kai, Yehohiyacin ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda, ka zama zoben hatimin dama a hannuna na dama, zan kwaɓe ka.

  9. Zan ba da kai ga waɗanda suke neman ranka, waɗanda kake tsoro, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da kuma ga Babiloniyawa.

  10. Zan jefar da kai da mahaifiyar da ta haife ka zuwa wata ƙasa, inda babu ɗayanku da aka haifa a wurin, a can kuma za ka mutu.

  11. zan kira dukan mutanen arewa da bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon,” in ji Ubangiji, “zan kuma kawo su su yi gāba da wannan ƙasa da mazaunanta da kuma gāba da dukan al’ummai da suke kewaye. Zan hallaka su sarai in kuma mai da su abin bantsoro da abin dariya, za su kuma zama kufai har abada.

  12. Zan kawar da muryoyin farin ciki da murna daga gare su, muryoyin amarya da na ango, ƙarar dutsen niƙa da hasken fitila.

  13. Dukan wannan ƙasa za tă zama kango, kuma waɗannan al’ummai za su bauta wa sarkin Babilon shekaru saba’in.