Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Babylon: The Jews exhorted to be subject to, and settle in

7 ayoyi · 73 fannoni

Ayoyi game da The Jews exhorted to be subject to, and settle in

  1. Ga abin da yake cikin wasiƙar annabi Irmiya da ya aika daga Urushalima zuwa ga sauran dattawan da suka ragu a cikin masu zaman bauta da kuma zuwa ga firistoci, annabawa da kuma dukan sauran mutanen da Nebukadnezzar ya kwashe zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon.

  2. (Wannan ya faru bayan Sarki Yekoniya da mahaifiyar sarauniya, shugabannin fada da kuma dukan shugabannin Yahuda da Urushalima, gwanayen sana’a da masu sassaƙa suka tafi zaman bauta daga Urushalima.)

  3. Ya ba da wasiƙar ta hannun Eleyasa ɗan Shafan da Gemariya ɗan Hilkiya, waɗanda Zedekiya sarkin Yahuda ya aika wurin Sarki Nebukadnezzar a Babilon. Wasiƙar ta ce,

  4. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ga dukan waɗanda aka kwashe zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon.

  5. “Ku gina gidaje ku zauna; ku dasa gonaki ku kuma ci abin da suka haifar.

  6. Ku yi aure ku kuma haifi ’ya’ya maza da mata; ku nemi mata wa ’ya’yanku maza, ku kuma ba da ’ya’yanku mata ga aure, saboda su ma za su haifi ’ya’ya maza da mata. Ku riɓaɓɓanya a can, kada ku ragu.

  7. Haka kuma, ku nemi zaman salama da cin gaba a birnin da aka kai ku zaman bauta. Ku yi addu’a ga Ubangiji saboda birnin, domin in ya ci gaba, ku ma za ku ci gaba.”