Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Babylon: Took Zedekiah, &c captive to Babylon

4 ayoyi · 73 fannoni

Ayoyi game da Took Zedekiah, &c captive to Babylon

  1. Babban hafsan ya kwashi Serahiya babban firist, da Zefaniya na biye da shi a girma, da matsara ƙofofi uku.

  2. Daga cikin waɗanda suka rage a birnin, ya ɗauki hafsa mai kula da dakaru, da kuma mashawartan sarki guda biyar. Ya kuma tafi da magatakarda wanda yake babban jami’in soja mai ɗaukan dukan jama’an ƙasar, tare da mutanensa guda sittin waɗanda aka samu a birnin.

  3. Nebuzaradan, babban hafsan, ya kwashe su duka ya kawo su wurin sarkin Babilon a Ribla.

  4. A can Ribla, a ƙasar Hamat, sarkin Babilon ya sa aka kashe su. Haka Yahuda ta tafi bauta daga ƙasarta.