Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Atonement: Unclassified scriptures relating to

91 ayoyi · 2 fannoni

Ayoyi game da Unclassified scriptures relating to

Tace bisa littafi
  1. Hadaya da sadaka ba ka sha’awa, amma kunnuwana ka huda; hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka bukata.

  2. Sa’an nan na ce, “Ga ni, na zo, kamar yadda yake a rubuce game da ni cikin littafi.

  3. Ina sha’awar aikata nufinka, ya Allahna; dokar tana cikin zuciyata.”

  4. Tabbatacce ya ɗauki cututtukanmu ya kuma daure da baƙin cikinmu duk da haka muka ɗauka Allah ya hukunta shi ne, ya buge shi ya kuma sa ya sha azaba.

  5. Amma aka yi masa rauni saboda laifofinmu, aka ƙuje shi saboda kurakuranmu; hukuncin da ya kawo mana salama ya kasance a kansa, kuma ta wurin mikinsa ya sa muka warke.

  6. Dukanmu, muna kama da tumakin da suka ɓata, kowannenmu ya kama hanyarsa; Ubangiji kuwa ya sa hukunci ya auko a kansa hukuncin da ya wajaba a kanmu.

  7. Aka wulaƙanta shi aka kuma yi masa azaba, duk da haka bai buɗe bakinsa ba; aka kai shi kamar ɗan rago zuwa wurin yanka, kuma kamar tunkiya a gaban masu askinta tana shiru, haka bai buɗe bakinsa ba.

  8. Da wulaƙanci da kuma hukunci aka ɗauke shi aka tafi. Wa kuwa zai yi maganar zuriyarsa? Gama an kawar da shi daga ƙasar masu rai; saboda laifin mutanena aka kashe shi.

  9. Aka yi jana’izarsa tare da mugaye, aka binne shi tare da masu arziki, ko da yake bai taɓa yin wani tashin hankali ba, ko a sami ƙarya a bakinsa.

  10. Duk da haka nufin Ubangiji ne a ƙuje shi yă kuma sa yă sha wahala, kuma ko da yake Ubangiji ya sa ransa ya zama hadaya don zunubi, zai ga zuriyarsa zai kuma kawo masa tsawon rai, nufin Ubangiji kuma zai yi nasara a hannunsa.

  11. Bayan wahalar ransa, zai ga hasken rai, ya kuma gamsu; ta wurin saninsa bawana mai adalci zai ’yantar da mutane masu yawa, zai kuma ɗauki laifofinsu.

  12. Saboda haka zan ba shi rabo tare da manya, zai kuma raba ganima tare da masu ƙarfi, domin ya ba da ransa har mutuwa, aka kuma lissafta shi tare da masu laifofi. Gama ya ɗauki zunubin mutane masu yawa, ya kuma yi roƙo saboda laifofinsu.

  13. “An ƙayyade wa jama’arka da tsattsarkan birninka shekara ɗari huɗu da tasa’in domin a kawo ƙarshen laifi da zunubi, domin a yi kafarar laifi, sa’an nan a shigo da adalci madawwami, a rufe wahayi da annabci, a tsarkake haikali.

  14. “Sai ka sani ka kuma fahimci wannan; Tun daga sa’ad da aka kafa doka don a maido a kuma sāke gina Urushalima har sai Shafaffen nan, mai mulki, ya zo, za a yi shekara arba’in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da mafaka.

  15. Bayan shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu, za a datse Shafaffen nan zai kuma kasance ba shi da kome. Mutanen mai mulkin za su zo su hallaka birnin da kuma wuri mai tsarki. Ƙarshen zai zo kamar rigyawa. Yaƙi zai ci gaba har ƙarshe, a kuma hallakar kamar yadda aka ƙaddara.

  16. Zai tabbatar da alkawari da mutane masu yawa har na shekara bakwai. A tsakiyar bakwai ɗin nan ɗaya zai kawo ƙarshen duk wata hadaya da baiko. Kuma a kusurwar haikali zai sa abin ƙyama mai kawo hallaka, har sai ƙarshen da aka ƙaddara ya auko wa wanda ya sa abin ƙyama.”

  17. Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da aka rubuta, cewa dole Kiristi yă sha wahala, a rana ta uku kuma yă tashi daga matattu.

  18. Kuma a cikin sunansa za a yi wa’azin tuba da gafarar zunubai, ga dukan ƙasashe. Za a kuwa fara daga Urushalima.

  19. Sai waninsu, mai suna Kayifas, wanda ya kasance babban firist a shekarar ya ce, “Ku dai ba ku san kome ba!

  20. Ba ku gane ba, ai, gwamma mutum ɗaya yă mutu saboda mutane da duk ƙasar ta hallaka.”

  21. Bai faɗa haka bisa nufinsa ba, sai dai a matsayinsa na babban firist a shekarar, ya yi annabci ne cewa Yesu zai mutu saboda ƙasar Yahudawa,

  22. Kamar yadda ya saba, Bulus ya shiga majami’ar, ranakun Asabbaci uku ya yi ta yin muhawwara da su daga cikin Nassosi,

  23. yana musu bayani da tabbatarwa cewa dole Kiristi ya sha wahala ya kuma tashi daga matattu. Ya kuma ce, “Wannan Yesu da nake sanar muku shi ne Kiristi.”

  24. an kuma kuɓutar da su kyauta ta wurin alherinsa bisa ga aikin fansar da ya zo ta wurin Yesu Kiristi.

  25. Allah ya miƙa Yesu Kiristi a matsayin hadayar kafara, ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya yi haka domin yă nuna adalcinsa, domin a cikin haƙurinsa bai hukunta zunuban da aka aikata a dā ba