- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1010–970 BC
The Reign of David
David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 1 Tarihi 29:1kusan 1015 K.H.
Sa’an nan Sarki Dawuda ya ce wa dukan taron, “Ɗana Solomon, wanda Allah ya zaɓa, matashi ne, kuma bai gogu ba. Aikin yana da yawa, domin wannan ƙasaitaccen ginin ba na mutum ba ne, na Ubangiji Allah ne.
- 1 Tarihi 29:2kusan 1015 K.H.
Na riga na tara dukan kayayyakin da na tanada saboda haikalin Allahna, zinariya saboda dukan ayyukan zinariya, azurfa saboda ayyukan azurfa, tagulla saboda ayyukan tagulla, ƙarfe saboda ayyukan ƙarfe da kuma katako saboda ayyukan katako, da onis don ado, turkuwoyis, duwatsu masu launi dabam-dabam, da kuma dukan duwatsu masu kyau da mabul, dukan waɗannan suna nan jingim.
- 1 Tarihi 29:3kusan 1015 K.H.
Ban da haka ma, cikin sa zuciyata ga haikalin Allahna, yanzu na ba da ma’ajina na zinariya da azurfa saboda haikalin Allahna, fiye da kome na tanada saboda wannan haikali,
- 1 Tarihi 29:4kusan 1015 K.H.
talenti dubu uku na zinariya (zinariyar Ofir) da tacecciyar azurfa dubu bakwai; don adon bangon gine-ginen,
- 1 Tarihi 29:5kusan 1015 K.H.
don aikin zinariya da kuma aikin azurfa, don kuma dukan aikin da gwanaye za su yi. Yanzu fa wa yake da niyya yă miƙa kansa a yau don Ubangiji?”
- 1 Tarihi 29:6kusan 1015 K.H.
Sai shugabannin iyalai, shugabannin kabilan Isra’ila, manyan hafsoshin mayaƙa dubu-dubu da manyan hafsoshi mayaƙa ɗari-ɗari, da shugabannin lura da ayyukan sarki suka yi bayarwa da yardar rai.
- 1 Tarihi 29:7kusan 1015 K.H.
Suka bayar talenti dubu biyar na zinariya, talenti dubu goma na azurfa, talenti dubu goma sha takwas na tagulla da talenti dubu ɗari na ƙarfe don aiki a haikalin Allah.
- 1 Tarihi 29:8kusan 1015 K.H.
Duk waɗanda suke da duwatsu masu daraja suka ba da su ga Yehiyel mutumin Gershon ma’ajin haikalin Ubangiji.
- 1 Tarihi 29:9kusan 1015 K.H.
Mutane suka yi farin ciki ganin yadda shugabanninsu suke bayarwa da yardar rai, gama sun bayar hannu sake da kuma dukan zuciya ga Ubangiji. Dawuda sarki shi ma ya yi farin ciki ƙwarai.
- 1 Tarihi 29:10kusan 1015 K.H.
Dawuda ya yabi Ubangiji a gaban dukan taron, yana cewa, “Yabo gare ka, ya Ubangiji, Allah na mahaifinmu Isra’ila, har abada abadin.
- 1 Tarihi 29:11kusan 1015 K.H.
Girma da iko da ɗaukaka, da daraja da kuma nasara naka ne, ya Ubangiji, gama kome a sama da ƙasa naka ne. Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji; an kuma ɗaukaka ka a matsayin kai a bisa duka.
- 1 Tarihi 29:12kusan 1015 K.H.
Wadata da girma daga gare ka suke; kai ne mai mulkin dukan abubuwa. A hannuwanka ne ƙarfi da iko suke don ka ɗaukaka da kuma ba da ƙarfi ga duka.
- 1 Tarihi 29:13kusan 1015 K.H.
Yanzu fa, Allahnmu, muna gode maka, muna kuma yabon ɗaukakar sunanka.
- 1 Tarihi 29:14kusan 1015 K.H.
“Amma wane ni, kuma wace ce jama’ata da za mu iya ba ka a yalwace kamar haka? Kome daga gare ka suka fito, kuma mun ba ka abin da kawai ya fito daga hannunka ne.
- 1 Tarihi 29:15kusan 1015 K.H.
Mu bare ne kuma baƙi a gabanka, kamar yadda dukan kakanninmu suke. Kwanakinmu a duniya suna kamar inuwa ne, ba sa zuciya.
- 1 Tarihi 29:16kusan 1015 K.H.
Ya Ubangiji Allahnmu, game da dukan wannan yalwar da ka tanada saboda ginin haikali saboda Sunanka Mai Tsarki, sun fito daga hannunka ne, kuma dukan naka ne.
- 1 Tarihi 29:17kusan 1015 K.H.
Na sani, Allahna, cewa kakan gwada zuciya, kakan kuma gamsu da mutunci. Dukan waɗannan abubuwa na bayar da yardar rai da kuma kyakkyawar niyya. Yanzu kuma da farin ciki na ga yadda mutanenka waɗanda suke a nan da yardar rai suka ba ka.
- 1 Tarihi 29:18kusan 1015 K.H.
Ya Ubangiji Allah na kakanninmu Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, ka sa wannan sha’awa a cikin zukatan mutanenka har abada, ka kuma bar zukatansu su yi maka biyayya.
- 1 Tarihi 29:19kusan 1015 K.H.
Ka kuma ba ɗana Solomon cikakkiyar zuciya don yă kiyaye umarnanka, farillanka da ƙa’idodinka yă kuma yi kome don yă gina ƙasaitaccen gini wanda na riga na yi tanadi dominsa.”
- 1 Tarihi 29:20kusan 1015 K.H.
Sa’an nan Dawuda ya ce wa dukan taron, “Ku yabi Ubangiji Allahnku.” Saboda haka suka yabi Ubangiji Allah na kakanninsu; suka rusuna suka kuma fāɗi rubda ciki a gaban Ubangiji da kuma sarki.
- 1 Tarihi 29:21kusan 1015 K.H.
Kashegari suka miƙa hadayu ga Ubangiji suka kuma miƙa hadayu bijimai dubu, raguna dubu da kuma ’yan raguna dubu na ƙonawa gare shi, tare da hadayunsu na sha da sauran hadayu a yalwace saboda dukan Isra’ila.
- 1 Tarihi 29:22kusan 1015 K.H.
Suka ci suka sha da farin ciki mai girma a gaban Ubangiji a wannan rana. Sa’an nan suka yarda da Solomon ɗan Dawuda a matsayin sarki sau na biyu, suka shafe shi a gaban Ubangiji don yă zama mai mulki, Zadok kuwa ya zama firist.
- 1 Tarihi 29:23kusan 1015 K.H.
Saboda haka Solomon ya zauna a kujerar sarautar Ubangiji a matsayin sarki a maimakon mahaifinsa Dawuda. Ya yi nasara, dukan Isra’ila kuwa suka yi masa biyayya.
- 1 Tarihi 29:24kusan 1015 K.H.
Dukan shugabanni da jarumawa, har ma da dukan ’ya’yan Sarki Dawuda maza, suka yi alkawari za su yi wa Sarki Solomon biyayya.
- 1 Tarihi 29:25kusan 1015 K.H.
Ubangiji ya ɗaukaka Solomon sosai a idon dukan Isra’ila, ya kuma ba shi darajar sarauta yadda babu sarki a Isra’ilan da ya taɓa samu.