Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Luka 6:24kusan 31 M.

    “Amma kaitonku da kuke da arziki, gama kun riga kun sami ta’aziyyarku.

  2. Luka 6:25kusan 31 M.

    Kaitonku da kuke ƙosassu yanzu, gama za ku zauna da yunwa. Kaitonku da kuke dariya yanzu, gama za ku yi makoki da kuka.

  3. Luka 6:26kusan 31 M.

    Kaitonku sa’ad da dukan mutane suna magana mai kyau a kanku, gama haka kakanninsu suka yi da annabawan ƙarya.

  4. Luka 6:27kusan 31 M.

    “Amma ina faɗa muku, ku da kuke ji na, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku yi wa masu ƙinku alheri.

  5. Luka 6:28kusan 31 M.

    Ku albarkaci waɗanda suke la’anta ku, ku kuma yi wa waɗanda suke wulaƙanta ku addu’a.

  6. Luka 6:29kusan 31 M.

    In wani ya mare ka a wannan kumatu, juya masa ɗayan ma, in wani ya ƙwace maka babban riga, kada ma ka hana masa ’yar cikin ma.

  7. Luka 6:30kusan 31 M.

    Duk wanda ya roƙe ka abu, ka ba shi. In kuma wani ya yi maka ƙwace, kada ka nema yă mayar maka.

  8. Luka 6:31kusan 31 M.

    Ka yi wa waɗansu abin da kai kake so su yi maka.

  9. Luka 6:32kusan 31 M.

    “In kana ƙaunar masu ƙaunarka ne kawai, ina ribar wannan? Ko masu zunubi ma suna ƙaunar waɗanda suke ƙaunarsu.

  10. Luka 6:33kusan 31 M.

    In kuma kana yin alheri ga masu yi maka ne kaɗai, ina ribar wannan? Ko masu zunubi ma suna yin haka.

  11. Luka 6:34kusan 31 M.

    In kana ba da bashi ga mutanen da za su iya biyan ka ne kawai, ina ribar wannan? Ko masu zunubi ma, suna ba da bashi ga masu zunubi, da fata za a biya su tsab.

  12. Luka 6:35kusan 31 M.

    Amma, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku kuma yi musu alheri, ku ba su bashi, ba da sa zuciya sai an biya ku ba. Ta yin haka ne kawai, za ku sami lada mai yawa, ku kuma zama ’ya’yan Mafi Ɗaukaka, gama shi mai alheri ne ga marasa godiya da mugaye.

  13. Luka 6:36kusan 31 M.

    Ku zama masu jinƙai, kamar yadda Ubanku mai jinƙai ne.

  14. Luka 6:37kusan 31 M.

    “Kada ku ɗora wa wani, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yanke wa wani hukunci, ku ma ba za a yanke muku ba. Ku gafarta, ku ma za a gafarta muku.

  15. Luka 6:38kusan 31 M.

    Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har yă yi tozo, yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna da shi, da shi za a auna muku.”

  16. Luka 6:39kusan 31 M.

    Ya kuma faɗa musu wannan misali cewa, “Makaho yana iya jagoran makaho ne? Ba sai dukansu biyu su fāɗa a rami ba?

  17. Luka 6:40kusan 31 M.

    Ɗalibi bai fi malaminsa ba, sai dai kowane ɗalibi wanda ya sami cikakkiyar koyarwa, zai zama kamar malaminsa.

  18. Luka 6:41kusan 31 M.

    “Don me kake duban ɗan tsinke da yake idon ɗan’uwanka, amma ba ka kula da gungumen da yake a naka ido ba?

  19. Luka 6:42kusan 31 M.

    Yaya za ka ce wa ɗan’uwanka, ‘Ɗan’uwa, bari in cire maka ɗan tsinke da yake idonka,’ alhali kuwa, kai kanka ka kāsa ganin gungumen da yake a naka ido? Kai munafuki! Ka fara cire gungumen daga idonka, sa’an nan za ka iya gani sosai, ka kuma cire ɗan tsinken da yake a idon ɗan’uwanka.”

  20. Luka 6:43kusan 31 M.

    “Ba itace mai kyau da yake ba da munanan ’ya’ya. Mummunan itace kuma ba ya ba da ’ya’ya masu kyau.

  21. Luka 6:44kusan 31 M.

    Kowane itace da irin ’ya’yansa ne ake saninsa. Mutane ba sa tsinke ’ya’yan ɓaure daga ƙaya, ko kuwa ’ya’yan inabi daga sarƙaƙƙiya.

  22. Luka 6:45kusan 31 M.

    Mutumin nagari yakan nuna abubuwa nagari daga cikin nagarta da yake a ɓoye a zuciyarsa, mugun mutum kuwa yakan nuna mugayen abubuwa daga muguntar da take a ɓoye a zuciyarsa. Gama baki yakan faɗa abin da ya cika zuciya ne.”

  23. Luka 6:46kusan 31 M.

    “Don me kuke ce da ni, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ amma ba kwa yin abin da na faɗa?

  24. Luka 6:47kusan 31 M.

    Zan nuna muku kwatancin mutumin da yakan zo wurina, yă ji kalmomina, yă kuma aikata.

  25. Luka 6:48kusan 31 M.

    Yana kama da mutumin da ya gina gida, wanda ya haƙa ƙasa da zurfi, sa’an nan ya kafa tushen ginin a kan dutse. Da ambaliyar ruwa ta taso, ƙarfin ruwa kuwa ya buga gidan, wannan bai jijjiga shi ba, domin an yi masa tushen gini na ainihi.