- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 800–400 BC
The Hebrew Prophets
God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Zakariya 5:3kusan 519 K.H.
Sai ya ce mini, “Wannan ce la’anar da za tă ratsa dukan ƙasar; gama bisa ga abin da ya ce a gefe ɗaya, za a kawar da kowane ɓarawo, kuma bisa ga abin da ya ce a ɗaya gefen za a kawar da duk mai rantsuwar ƙarya.
- Zakariya 5:4kusan 519 K.H.
Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Zan aika shi, zai shiga gidan ɓarawo, da gidan mai rantsuwar ƙarya da sunana. Zai kasance a gidansa yă hallaka gidan da katakon da duwatsun.’ ”
- Zakariya 5:5kusan 519 K.H.
Sai mala’ikan da yake mini magana ya zo gaba ya ce mini, “Duba ka gani ko mene ne wannan da yake fitowa.”
- Zakariya 5:6kusan 519 K.H.
Na tambaya na ce, “Mene ne?” Ya amsa ya ce, “Kwando ne na awo.” Ya ƙara da cewa, “Wannan shi ne laifin mutanen a duk fāɗin ƙasar.”
- Zakariya 5:7kusan 519 K.H.
Sa’an nan aka ɗaga murfin dalman, a ciki kuwa ga mace zaune!
- Zakariya 5:8kusan 519 K.H.
Ya ce, “Wannan mugunta ce,” ya kuma tura ta cikin kwandon ya rufe da murfin dalman, ya kuma danna da dutse.
- Zakariya 5:9kusan 519 K.H.
Na ɗaga idona sama, sai ga mata biyu a gabana, iska tana hura fikafikansu! Suna da fikafikai kamar na shamuwa, suka kuma ɗaga kwandon sama.
- Zakariya 5:10kusan 519 K.H.
Na tambayi mala’ikan da yake magana da ni na ce, “Ina za ku kai kwandon?”
- Zakariya 5:11kusan 519 K.H.
Ya amsa ya ce, “Zuwa ƙasar Babiloniya don a gina masa haikali. Sa’ad da aka gama ginin, za a ajiye shi a ciki.”
- Zakariya 6:1kusan 519 K.H.
Na sāke ɗaga kai sama, sai ga kekunan yaƙi guda huɗu a gabana suna fitowa tsakanin duwatsu guda biyu, duwatsun tagulla!
- Zakariya 6:2kusan 519 K.H.
Karusa ta farko tana da jajjayen dawakai, ta biyu kuma baƙaƙen dawakai,
- Zakariya 6:3kusan 519 K.H.
ta ukun farare dawakai, ta huɗu kuma dawakai masu ɗigo-ɗigo a dukan jikinsu, dukansu kuwa ƙarfafa.
- Zakariya 6:4kusan 519 K.H.
Sai na tambayi mala’ikan da yake magana da ni na ce, “Mene ne waɗannan, ranka yă daɗe?”
- Zakariya 6:5kusan 519 K.H.
Mala’ikan ya amsa mini ya ce, “Waɗannan su ne ruhohi huɗu na sama, waɗanda suka fito daga wurin Ubangiji na dukan duniya.
- Zakariya 6:6kusan 519 K.H.
Wannan mai baƙaƙen dawakai zai nufi wajen ƙasar arewa, mai fararen dawakai zai nufi wajen yamma, sai kuma mai dawakai masu ɗigo-ɗigo a jiki zai nufi wajen kudu.”
- Zakariya 6:7kusan 519 K.H.
Da ƙarfafa dawakan suka fito, sai suka yi marmari su ratsa dukan duniya. Sai ya ce, “Ku ratsa dukan duniya!” Saboda haka suka ratsa dukan duniya.
- Zakariya 6:8kusan 519 K.H.
Sai ya kira ni ya ce, “Duba, waɗanda suka nufi wajen ƙasar arewa sun ba wa Ruhuna hutu a ƙasar arewa.”
- Zakariya 6:9kusan 519 K.H.
Maganar Ubangiji ta zo mini, ta ce,
- Zakariya 6:10kusan 519 K.H.
“Ka karɓi azurfa da zinariya daga masu zaman bauta Heldai, Tobiya, Yedahiya, waɗanda suka iso daga Babilon. A ranar kuma ka je gidan Yosiya ɗan Zefaniya.
- Zakariya 6:11kusan 519 K.H.
Ka ɗauki azurfar da zinariyar ka yi rawani, ka ɗora shi a kan babban firist, Yoshuwa ɗan Yehozadak.
- Zakariya 6:12kusan 519 K.H.
Ka ce masa ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ga mutumin da sunansa ne Reshe, zai kuma ratse daga inda yake yă gina haikalin Ubangiji.
- Zakariya 6:13kusan 519 K.H.
Shi ne zai gina haikalin Ubangiji, za a kuma martaba shi da daraja, zai kuma zauna yă yi mulki a kan kursiyinsa. Zai zama firist a kan kursiyinsa. Kuma a tsakanin biyun za a sami zaman lafiya.’
- Zakariya 6:14kusan 519 K.H.
Za a ba Heldai, Tobiya, Yedahiya da kuma Hen ɗan Zefaniya kamar abin tunawa a cikin haikalin Ubangiji.
- Zakariya 6:15kusan 519 K.H.
Waɗanda suke nesa za su zo su taimaka gina haikalin Ubangiji, za ku kuma san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni gare ku. Wannan zai faru in kuka yi biyayya sosai ga Ubangiji Allahnku.”
- Zakariya 7:1kusan 518 K.H.
A shekara ta huɗu ta Sarki Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa Zakariya a rana ta huɗu ta watan tara, wato, watan Kisleb.