Tsallake zuwa abun ciki

circa 605–538 BC

The Babylonian Exile

Jerusalem falls and the temple burns; Ezekiel and Daniel minister among the exiles as Lamentations mourns the city's ruin.

1,784 ayoyi · 3 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ezekiyel 33:6kusan 587 K.H.

    Amma a ce mai tsaron ya ga takobi yana zuwa bai kuwa busa ƙaho don yă faɗakar da mutane ba sai takobi ya zo ya ɗauki ran waninsu, za a kawar da wannan mutum saboda zunubinsa, amma zan nemi hakkin jinin mutumin a kan mai tsaron.’

  2. Ezekiyel 33:7kusan 587 K.H.

    “Ɗan mutum, na mai da kai mai tsaro bisa gidan Isra’ila; saboda haka ka ji abin da zan faɗa ka kuma gargaɗe su.

  3. Ezekiyel 33:8kusan 587 K.H.

    Sa’ad da na ce wa mugu, ‘Ya mugun mutum, tabbatacce za ka mutu,’ kai kuma ba ka yi magana don ka juyar da shi daga hanyoyinsa ba, wannan mugun mutum zai mutu domin zunubinsa, zan kuma nemi hakkin jininsa a kanka.

  4. Ezekiyel 33:9kusan 587 K.H.

    Amma in ka faɗakar da mugun mutumin don yă juye daga hanyoyinsa bai kuwa yi haka ba, zai mutu saboda zunubinsa, amma kai za ka kuɓutar da kanka.

  5. Ezekiyel 33:10kusan 587 K.H.

    “Ɗan mutum, faɗa wa gidan Isra’ila, ‘Ga abin da kuke cewa, “Laifofinmu da zunubanmu suna nawaita mana, muna kuma lalacewa saboda su. Ta ƙaƙa za mu rayu?” ’

  6. Ezekiyel 33:11kusan 587 K.H.

    Ka faɗa musu, ‘Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba na jin daɗin mutuwar mugu, amma a maimako haka ya fi su juye daga hanyoyinsu su rayu. Ku juye! Ku juye daga mugayen hanyoyinku! Don me za ku mutu, ya gidan Isra’ila?’

  7. Ezekiyel 33:12kusan 587 K.H.

    “Saboda haka, ɗan mutum, ka faɗa wa mutanen ƙasarka, ‘Adalcin adali ba zai cece shi sa’ad da ya ƙi yin biyayya ba, kuma muguntar mugu ba za tă sa ya fāɗi sa’ad da ya juya daga gare ta ba. Adali, in ya yi zunubi, ba za a bari yă rayu saboda adalcinsa na dā ba.’

  8. Ezekiyel 33:13kusan 587 K.H.

    In na faɗa wa adali cewa tabbatacce zai rayu, amma sai ya dogara ga adalcinsa ya kuma aikata mugunta, babu ayyukan adalcinsa da za a tuna; zai mutu saboda muguntar da ya aikata.

  9. Ezekiyel 33:14kusan 587 K.H.

    Kuma in na ce wa mugu, ‘Tabbatacce za ka mutu,’ amma sai ya juye daga zunubinsa ya kuma yi abin da yake gaskiya da kuma daidai,

  10. Ezekiyel 33:15kusan 587 K.H.

    in ya mayar da jingina, ya mayar da abin da ya sata, ya kiyaye ƙa’idodin da suke ba da rai, ya daina yin mugunta, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba.

  11. Ezekiyel 33:16kusan 587 K.H.

    Babu wani zunubin da ya aikata da za a tuna da shi. Ya yi abin da yake gaskiya da kuma daidai; tabbatacce zai rayu.

  12. Ezekiyel 33:17kusan 587 K.H.

    “Duk da haka mutanen ƙasarka sun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Alhali kuwa tasu ce ba daidai ba.

  13. Ezekiyel 33:18kusan 587 K.H.

    In adali ya juye daga adalcinsa ya yi mugunta, zai mutu saboda haka.

  14. Ezekiyel 33:19kusan 587 K.H.

    Kuma in mugu ya juye daga muguntarsa ya aikata abin da yake gaskiya da kuma daidai, zai rayu ta yin haka.

  15. Ezekiyel 33:20kusan 587 K.H.

    Duk da haka, ya gidan Isra’ila kun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Amma zan hukunta kowane ɗayanku gwargwadon ayyukansa.”

  16. Ezekiyel 33:21kusan 587 K.H.

    A shekara ta goma sha biyu ta zaman bautanmu, a wata na goma a rana ta biyar, wani mutumin da ya gudu daga Urushalima ya zo wurina ya ce, “Birnin ya fāɗi!”

  17. Ezekiyel 33:22kusan 587 K.H.

    To a yamman da ya wuce kafin mutumin ya iso, hannun Ubangiji yana a kaina, ya kuma buɗe bakina kafin mutumin ya iso wurina da safe. Sai bakina ya buɗu ban kuma yi shiru ba.

  18. Ezekiyel 33:23kusan 587 K.H.

    Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  19. Ezekiyel 33:24kusan 587 K.H.

    “Ɗan mutum, mutanen da suke zama a waɗannan kufai a ƙasar Isra’ila suna cewa, ‘Ibrahim mutum ɗaya ne kaɗai, duk da haka Ibrahim ya mallaki ƙasar. Amma mu da muke da yawa; lalle an ba mu ƙasar ta zama mallakarmu.’

  20. Ezekiyel 33:25kusan 587 K.H.

    Saboda haka ka faɗa musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa da yake kun ci nama da jini a cikinsa kuka kuma bauta wa gumakanku kuka zub da jini, kuna gani za ku mallaki ƙasar?

  21. Ezekiyel 33:26kusan 587 K.H.

    Kun dogara ga takobinku, kuka aikata abubuwan banƙyama, kowannenku kuma ya ƙazantar da matar maƙwabcinsa. Kuna gani za ku mallaki ƙasar?’

  22. Ezekiyel 33:27kusan 587 K.H.

    “Ka faɗa musu wannan, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa muddin ina raye, waɗanda aka rage a kufai za su fāɗi ga takobi, waɗanda suke bayan gari kuwa namun jeji za su cinye su, waɗanda suke a mafaka da kogwannin duwatsu annoba za tă kashe su.

  23. Ezekiyel 33:28kusan 587 K.H.

    Zan mai da ƙasar kango, kuma fariyar ƙarfinta zai ƙare, duwatsun Isra’ila za su zama kufai don kada wani ya ratsa su.

  24. Ezekiyel 33:29kusan 587 K.H.

    Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na mai da ƙasar kango saboda dukan abubuwan banƙyamar da suka yi.’

  25. Ezekiyel 33:30kusan 587 K.H.

    “Game da kai kuma, ɗan mutum, mutanen ƙasarka suna magana da juna game da kai a katanga da kuma ƙofofin gidaje, suna ce wa juna, ‘Ku zo mu tafi mu ji maganar da ta zo daga wurin Ubangiji.’