Tsallake zuwa abun ciki

John

89 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci John

Tace bisa littafi
  1. Yesu ya ji labari cewa Yahudawa sun ji cewa ya wuce Yohanna samun masu bi, yana kuma yin musu baftisma,

  2. “Kun aika wajen Yohanna ya kuma yi shaida a kan gaskiya.

  3. “Ina da shaidar da ta fi ta Yohanna ƙarfi. Gama aikin nan da Uba ya ba ni in kammala, wanda kuwa nake yi, yana ba da shaida cewa Uba ne ya aiko ni.

  4. Sa’an nan Yesu ya sāke koma ƙetaren Urdun inda dā Yohanna yake baftisma. A can ya zauna

  5. mutane da yawa suka zo wurinsa. Suka ce, “Ko da yake Yohanna bai yi wani abin banmamaki ba, duk abubuwan da Yohanna ya faɗa game da mutumin nan gaskiya ne.”

  6. Gama Yohanna ya yi baftisma daruwa, amma a cikin ’yan kwanaki za a yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.”

  7. farawa daga baftisma ta Yohanna har zuwa sa’ad da aka ɗauke Yesu daga gare mu. Gama dole ɗaya daga waɗannan ya zama shaidar tashinsa daga matattu tare da mu.”

  8. Kun san abin da ya faru a dukan Yahudiya, farawa daga Galili bayan baftismar da Yohanna ya yi wa’azi,

  9. Sa’an nan na tuna da abin da Ubangiji ya ce, ‘Yohanna ya yi baftisma da ruwa, amma za a yi muku baftisma daRuhu Mai Tsarki.’

  10. Kafin zuwan Yesu, Yohanna ya yi wa’azin tuba da baftisma ga dukan mutanen Isra’ila.

  11. Yayinda Yohanna yake kammala aikinsa ya ce, ‘Wa kuke tsammani ni nake? Ba ni ne shi ba. A’a, amma yana zuwa bayana, wanda ko takalmansa ma ban isa in kunce ba.’

  12. An horar da shi a hanyar Ubangiji, ya kuma himma ƙwarai a magana, ya kuma yi koyarwa game da Yesu, daidai, ko da yake baftismar Yohanna ce kaɗai ya sani.

  13. Saboda haka Bulus ya yi tambaya ya ce, “To, wace baftisma aka yi muku?” Suka ce, “Baftismar Yohanna.”

  14. Bulus ya ce, “Ai, baftismar Yohanna, baftisma ce ta tuba. Ya ce wa mutane su gaskata a wani wanda yake zuwa bayansa, wato, Yesu.”