Tsallake zuwa abun ciki

Elisabeth

8 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Elisabeth

  1. A lokacin da Hiridus ne yake sarautar Yahudiya, an yi wani firist mai suna Zakariya, na sashin firistoci gidan Abiya. Matarsa Elizabet ma ’yar zuriyar Haruna ce.

  2. Sai dai ba su da ’ya’ya, domin Elizabet bakararriya ce; kuma dukansu biyu sun tsufa.

  3. Amma mala’ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, Zakariya; an ji addu’arka. Matarka Elizabet za tă haifa maka ɗa, za ka kuma ba shi suna Yohanna.

  4. Bayan wannan, matarsa Elizabet ta yi ciki, ta kuma riƙa ɓuya har wata biyar.

  5. ’Yar’uwarki Elizabet ma za tă haifi ɗa a tsufanta, ita da aka ce bakararriya, ga shi tana a watanta na shida.

  6. inda ta shiga gidan Zakariya ta kuma gai da Elizabet.

  7. Da Elizabet ta ji gaisuwar Maryamu, sai jaririn da yake a cikinta ya yi motsi. Elizabet kuma ta cika da Ruhu Mai Tsarki.

  8. Sa’ad da kwanaki suka yi don Elizabet ta haihu, sai ta haifi ɗa.