Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prophetesses

18 ayoyi · 10 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Sa’an nan Miriyam annabiya, ’yar’uwar Haruna ta ɗauki ganga a hannunta, dukan mata kuwa suka bi ta, da ganguna suna rawa.

  2. A lokacin Debora annabiya, matar Laffidot ce take bi da Isra’ila.

  3. Sai Hilkiya firist, da Ahikam, Akbor, da Shafan, da kuma Asahiya suka je don su yi magana da annabiya Hulda, matan Shallum ɗan Tikba, ɗan Harhas, mai ajiyar tufafi. Tana zama a Urushalima, a Yanki na Biyu.

  4. Ya Allahna, ka tuna da Tobiya da Sanballat, saboda abin da suka yi; ka kuma tuna da annabiya Nowadiya da sauran annabawa waɗanda suke ƙoƙari su tsorata ni.

  5. Sa’an nan na tafi na yi jima’i da annabiya, ta kuwa yi ciki ta haifi ɗa. Ubangiji kuma ya ce mini, “Raɗa masa suna, Maher-Shalal-Hash-Baz.

  6. “To, ɗan mutum, ka kafa idonka a kan ’yan matan mutanenka waɗanda suke annabci bisa ga ra’ayinsu. Yi annabci a kansu

  7. “Daga baya kuma, zan zuba Ruhuna a bisan dukan mutane. ’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci, tsofaffinku za su yi mafarkai, matasanku za su ga wahayoyi.

  8. Har ma a bisan bayina, maza da mata, zan zuba Ruhuna a kwanakin nan.

  9. Da Elizabet ta ji gaisuwar Maryamu, sai jaririn da yake a cikinta ya yi motsi. Elizabet kuma ta cika da Ruhu Mai Tsarki.

  10. Sai ta ɗaga murya da ƙarfi ta ce, “Ke mai albarka ce a cikin mata. Mai albarka ne kuma ɗan da za ki haifa!

  11. Me ya sa na sami wannan tagomashi har da mahaifiyar Ubangijina za tă zo wurina?

  12. Da jin gaisuwarki, sai jaririn da yake cikina ya yi motsi don murna.

  13. Mai albarka ce wadda ta gaskata cewa abin da Ubangiji ya faɗa mata zai cika!”

  14. Akwai wata annabiya ma, mai suna Anna, diyar Fanuwel, na kabilar Asher. Ta tsufa kutuf; ta yi zama da mijinta shekaru bakwai bayan sun yi aure,

  15. ta kuwa zama gwauruwa sai da ta kai shekaru tamanin da huɗu. Ba ta taɓa barin haikali ba, tana sujada dare da rana, tana kuma azumi da addu’a.

  16. Tana haurawa wurinsu ke nan a wannan lokaci, sai ta yi wa Allah godiya ta kuma yi magana game da yaron nan ga dukan waɗanda suke sauraron fansar Urushalima.

  17. Yana da ’ya’ya huɗu ’yan mata da ba su yi aure ba, waɗanda suka yi annabci.

  18. Duk da haka, ina da wannan game da kai. Kana haƙuri da matan nan Yezebel, wadda take kira kanta annabiya. Ta wurin koyarwarta tana ɓad da bayina ga yin fasikanci suka kuma ci abincin da aka miƙa wa gumaka.