Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Amma saboda su, zan tuna da alkawarin da na yi da kakanninsu, waɗanda na fitar da su daga Masar a idon al’ummai, don in zama Allahnsu. Ni ne Ubangiji.’ ”

  2. Waɗannan su ne farillai, da dokoki, da kuma ƙa’idodin da Ubangiji ya kafa a Dutsen Sinai, tsakaninsa da Isra’ilawa ta wurin Musa.

  3. Ubangiji ya ce wa Musa,

  4. “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Duk sa’ad da mutum ya yi rantsuwa ta musamman zai keɓe wani ga Ubangiji, ta wurin biyan kuɗaɗen fansa,

  5. “ ‘In abin da ya yi alkawarin yardajje ne a matsayin hadaya ga Ubangiji, wannan dabbar da aka bayar ga Ubangiji, za tă zama mai tsarki.

  6. In abin da ya yi alkawari dabba ce marar tsarki, wadda ba yardajje ba ce, a matsayin hadaya ga Ubangiji, dole a kai dabbar wa firist,

  7. “ ‘In mutum ya miƙa gidansa a matsayin wani abu mai tsarki ga Ubangiji, firist zai daidaita dacewar ko mai kyau ne, ko marar kyau. Duk darajar da firist ya kimanta, haka za tă zama.

  8. “ ‘In wani ya keɓe wa Ubangiji wani sashe daga cikin gonarsa ta gādo, sai yă kimanta kuɗin gonar daidai da yawan irin da za a iya shuka a gonar. Za a kimanta kuɗin a kan shekel hamsin na irin sha’ir.

  9. Sa’ad da aka saki gonar a Shekara ta Murna, za tă zama mai tsarki, a matsayin gonar da aka miƙa ga Ubangiji, za tă zama mallakar firistoci.

  10. “ ‘In mutum ya keɓe gonar da ya saya, wadda take ba sashe na gonar iyali ba, ga Ubangiji,

  11. firist zai kimanta darajarta har Shekara ta Murna, dole kuma mutumin yă biya darajarta a ranar, a matsayin wani abu mai tsarki ga Ubangiji.

  12. “ ‘Ba wani da zai iya keɓe ɗan farin dabba, da yake ɗan fari ya riga ya zama na Ubangiji, ko na saniya, ko na tunkiya, na Ubangiji ne.

  13. “ ‘Amma babu abin da mutum ya mallaka, ya kuma keɓe ga Ubangiji, ko mutum ne, ko dabba, ko ganar iyali da za a sayar, ko a fansa; kome da aka keɓe a wannan hanya, mafi tsarki ne ga Ubangiji.

  14. “ ‘Ushirin kome daga gona, ko hatsi daga ƙasa, ko ’ya’yan itatuwa daga itatuwa, na Ubangiji ne, mai tsarki ne ga Ubangiji.

  15. Ushirin gaba ɗaya na garken shanu, da na tumaki, kowane kashi ɗaya bisa goma na dabbar da ta wuce ƙarƙashin sandan mai kiwo, za tă zama mai tsarki ga Ubangiji.

  16. Waɗannan su ne dokokin da Ubangiji ya ba wa Musa a Dutsen Sinai saboda Isra’ilawa.

  17. Ubangiji ya yi magana da Musa a Tentin Sujada a cikin Hamadar Sinai, a rana ta fari na watan biyu a shekara ta biyu, bayan Isra’ilawa suka fito Masar ya ce,

  18. yadda Ubangiji ya umarci Musa. Da haka ya ƙidaya su a Hamadar Sinai.

  19. Ubangiji ya riga ya gaya wa Musa cewa,

  20. Isra’ilawa suka yi duk waɗannan kamar dai yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  21. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

  22. Ba a dai ƙidaya Lawiyawa tare da sauran Isra’ilawa ba yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  23. Saboda haka Isra’ilawa suka yi duk ko mene ne da Ubangiji ya umarci Musa. Ta haka ne suka yi sansani a ƙarƙashin ƙa’idarsu kowanne tare da kabilarsa da danginsa.

  24. Waɗannan su ne zuriyar Haruna da Musa a lokacin da Ubangiji ya yi magana da Musa a kan Dutsen Sinai.

  25. Amma Nadab da Abihu suka fāɗi suka mutu a gaban Ubangiji a Hamadar Sinai a sa’ad da suka ƙona turare da haramtacciyar wuta a gabansa. Ba su kuwa da ’ya’ya; saboda haka Eleyazar da Itamar kaɗai suka yi aiki firist a zamanin mahaifinsu Haruna.