Markus 15:19-43
19
Suka dinga bugunsa a kā da sanda, suka tattofa masa miyau. Suka durƙusa suka yi masa bangirma na ba’a.
20
Bayan da suka gama yin masa ba’a, suka tuɓe rigar mai ruwan shunayyar, suka sa masa nasa tufafi. Sai suka tafi da shi don a gicciye shi.
21
Sai ga wani mutum daga Sairin da ake kira Siman, mahaifin Alekzanda da Rufus, yana wucewa kan hanyarsa daga ƙauye. Sai suka tilasta shi yă ɗauki gicciyen.
22
Suka kawo Yesu a wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai).
23
Sai suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da mur, don yă rage zafi, amma bai sha ba.
24
Sai suka gicciye shi. Suka rarraba tufafinsa, suka jefa ƙuri’a a kansu don su ga abin da kowa zai samu.
25
Sa’a ta uku na safe ce kuwa aka gicciye shi.
26
Akwai rubutu na zarginsa, da ya ce, Sarkin Yahudawa.
27
Suka gicciye ’yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗayan kuma a hagunsa.
29
Masu wucewa suka zazzage shi. Suka kaɗa kai suna cewa, “To, kai da za ka rushe haikali ka kuma gina shi a kwana uku,
30
sai ka sauko daga gicciyen, ka ceci kanka!”
31
Haka kuma, manyan firistoci da malaman dokoki suka yi masa ba’a a junansu, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa!
32
Bari wannan Kiristi, wannan Sarkin Isra’ila, yă sauko yanzu daga gicciye, don mu ga mu kuma gaskata.” Waɗanda aka gicciye tare da shi ma suka zazzage shi.
33
Daga sa’a ta shida har zuwa sa’a ta tara na rana, duhu ya rufe dukan ƙasar.
34
A daidai sa’a ta tara na rana, sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”).
35
Da waɗansu cikin waɗanda suke tsattsaye kusa da wurin suka ji haka, suka ce, “Ku saurara, yana kiran Iliya.”
36
Wani mutum ya ruga ya je ya jiƙo soso da ruwan tsami, ya soka a sanda ya miƙa wa Yesu yă sha. Ya ce, “Ku ƙyale shi. Bari mu ga ko Iliya zai zo yă saukar da shi.”
37
Da murya mai ƙarfi, Yesu ya ja numfashinsa na ƙarshe.
38
Labulen haikali kuwa ya yage kashi biyu, daga sama har ƙasa.
39
Da jarumin da yake tsaye a gaban Yesu ya ji muryarsa, ya kuma ga yadda ya mutu, sai ya ce, “Gaskiya, wannan mutum Ɗan Allah ne!”
40
Waɗansu mata suna kallo daga nesa. A cikinsu kuwa akwai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub ƙarami da Yusuf, da kuma Salome.
41
A Galili waɗannan mata ne suka riƙa bin sa suna yin masa hidima. Waɗansu mata da yawa da suka zo tare da shi daga Urushalima, su ma suna nan a can.
42
Ranar kuwa ita ce ranar Shirye-shirye (wato, ana kashegari Asabbaci). Saboda haka, da yamma ta yi, sai
43
Yusuf daga Arimateya, wani sanannen ɗan Majalisa, wanda dā ma yake jiran zuwan mulkin Allah, ya je wajen Bilatus ba tsoro, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.
Settings