Skip to content
Mahukunta 20:6-30

Mahukunta 20:6-30

6
Na ɗauki ƙwarƙwarata na yayyanka gunduwa-gunduwa na aika da shi ga kowane yankin gādon Isra’ila, domin sun aikata mugu abu da abin kunya a Isra’ila.
7
To, dukanku Isra’ilawa, sai ku yi magana ku kuma yanke hukuncinku.”
8
Dukan mutane suka tashi kamar mutum ɗaya, suna cewa “Ba waninmu da zai tafi gida. Sam, babu ko ɗayanmu da zai koma gidansa.
9
Amma yanzu ga abin da za mu yi wa Gibeya. Za mu haura mu fāɗa yadda ƙuri’a ta nunar.
10
Za mu ɗauko mutum goma a kowane mutum ɗari daga dukan kabilan Isra’ila, da ɗari a dubu, da kuma dubu a dubu goma, domin a tanada wa mayaƙan. Sa’an nan, sa’ad da mayaƙan suka iso Geba a Benyamin, za su yi da su daidai bisa ga muguntar da suka yi a Isra’ila.”
11
Saboda haka dukan mutane Isra’ilawa suka taru suka kuma haɗu kamar mutum guda don su fāɗa wa birnin da yaƙi.
12
Kabilan Isra’ila suka aika jakadu a ko’ina a cikin kabilar Benyamin cewa, “Wace irin mugunta ce wannan da kuka aikata?
13
Yanzu fa sai ku fitar da waɗannan ’yan iskan da suka aikata wannan abu na Gibeya don mu kashe su mu kawar da mugunta daga Isra’ila!” Amma mutanen Benyamin ba su saurari ’yan’uwansu Isra’ilawa ba.
14
Daga biranensu suka tattaru a Gibeya don su yaƙi Isra’ilawa.
15
Nan da nan mutanen Benyamin suka tattara mayaƙa dubu ashirin da shida masu takuba daga biranensu, ban da mayaƙa ɗari bakwai da aka zaɓa daga mazauna a Gibeya.
16
Cikin dukan mayaƙan nan akwai zaɓaɓɓu mutane ɗari bakwai waɗanda su bahagwai ne, kowanne yana iya harbin gashin guda na kai da majajjawa ba kuskure.
17
Isra’ila kuwa, ban da Benyamin, sun tara mayaƙa masu takobi dubu ɗari huɗu, dukansu gwanayen yaƙi ne.
18
Sai Isra’ilawa suka haura zuwa Betel suka nemi nufin Allah, suka ce, “Wane ne a cikinmu zai fara fāɗa wa mutanen Benyamin?” Ubangiji ya ce, “Yahuda ce za tă fara.”
19
Kashegari sai Isra’ilawa suka tashi suka kafa sansani kusa da Gibeya.
20
Mutanen Isra’ila suka fita yaƙi da mutane Benyamin suka kuma ja dāgār yaƙi a Gibeya.
21
Mutanen Benyamin suka fito daga Gibeya suka kashe mutum dubu ashirin da biyu na Isra’ilawa a dāgār yaƙi a ranar.
22
Amma mutanen Isra’ila suka ƙarfafa juna, suka sāke koma inda suka ja dāgā a rana ta farko.
23
Isra’ilawa suka haura suka yi kuka a gaban Ubangiji, har yamma, suka nemi nufin Ubangiji. Suka ce, “Mu sāke koma yaƙi da mutanen Benyamin, ’yan’uwanmu?” Ubangiji ya ce, “Ku haura ku fāɗa musu.”
24
Sai Isra’ilawa suka matsa kusa da Benyamin a rana ta biyu.
25
A wannan lokaci, da mutanen Benyamin suka fito daga Gibeya don su yaƙe su, sai suka sāke kashe Isra’ilawa dubu goma sha takwas, dukansu ɗauke da takuba.
26
Sa’an nan Isra’ilawa, dukan mutane, suka haura zuwa Betel, a can suka zauna suna kuka a gaban Ubangiji. Suka yi azumi a wannan rana har yamma suka miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama ga Ubangiji.
27
Isra’ilawa suka nemi nufin Ubangiji (A kwanakin nan akwatin alkawarin Allah yana can,
28
Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, kuwa yana hidima a gabansa.) Suka ce, “Mu sāke haura mu yi yaƙi da mutanen Benyamin ’yan’uwanmu, ko a’a?” Ubangiji ya ce, “Ku je, gama gobe zan ba da su a hannuwanku.”
29
Sa’an nan Isra’ila ta yi kwanto kewaya da Gibeya.
30
Suka haura su kara da mutanen Benyamin a rana ta uku suka ja dāgā a Gibeya kamar dā.

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.

Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options