Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wheat

11 ayoyi · 8 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. “Na ba ka duk man zaitun mafi kyau, da ruwan inabi mafi kyau duka, da hatsi mafi kyau duka na nunan farinsu da suke bayarwa ga Ubangiji.

  2. Solomon kuma ya ba wa Hiram mudu gari dubu ashirin na alkama a matsayin abinci domin gidansa, ya ƙara da garwa dubu ashirin na tataccen man zaitun. Solomon ya ci gaba da yin haka ga Hiram, shekara-shekara.

  3. Amma za a ciyar da ku da alkama mafi kyau; da zuma daga dutsen da zai ƙosar da ku.”

  4. Yana ba da salama ga iyakokinki yana kuma ƙosar da ke da alkama mafi kyau.

  5. Ko da ka daka wawa a turmi, kana daka shi kamar hatsi da taɓarya, ba za ka fid da wauta daga gare shi ba.

  6. Bari annabin da ya yi mafarki ya faɗa mafarkinsa, amma bari wanda yake da maganata ya yi ta da aminci. Gama me ya haɗa ciyawa da alkama?” In ji Ubangiji.

  7. Yana riƙe da matankaɗinsa, zai tankaɗe hatsinsa, yă kuma tattara alkamarsa a cikin rumbu, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.”

  8. Amma yayinda kowa yake barci, abokin gābansa ya zo ya yafa ciyayi a cikin alkamar, ya tafi abinsa.

  9. Matankaɗinsa yana a hannunsa don yă tankaɗe sussukarsa ya kuma tattara alkama cikin rumbunsa, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.”

  10. “Ya kuma tambayi na biyun, ‘Kai fa, nawa ne ake bin ka?’ “Sai ya amsa ya ce, ‘Buhunan alkama dubu.’ “Ya ce, ‘Ga takardarka, ka mai da shi ɗari takwas.’

  11. Sai na ji wani abu mai ƙara kamar wata murya a tsakiyar halittu huɗun nan masu rai tana cewa, “Kwatan alkama don albashin aikin yini, da kuma kwata uku na sha’ir don albashin yini guda, kada kuwa ka ɓata man da ruwan inabi!”