Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Washing: Figurative of regeneration

8 ayoyi · 2 fannoni

Ayoyi game da Figurative of regeneration

  1. Ka tsarkake ni da hizzob, zan kuwa zama tsab; ka wanke ni, zan kuma fi dusan ƙanƙara fari.

  2. waɗanda sukan ɗauka su tsarkaka ne a ganinsu alhali kuwa ƙazamai ne su;

  3. Ku yi wanka ku kuma tsabtacce kanku. Ku kawar da mugayen ayyukanku daga gabana; Ku daina aikata mugunta.

  4. Ubangiji zai wanke duk wani ƙazantar matan Sihiyona; ya tsabtacce jinin da aka zubar daga Urushalima ta wurin ruhun hukunci da yake ƙuna kamar wuta.

  5. “A ranan nan za a buɗe maɓulɓulan ruwa zuwa gidan Dawuda da mazaunan Urushalima, don a tsarkake su daga zunubi da rashin tsabta.

  6. Haka waɗansu a cikinku ma suke a dā. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, aka kuma sa kuka zama marasa laifi cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.

  7. Ya mai da ikkilisiya ta zama mai tsarki ta wurin ikon maganarsa, ya kuma tsabtacce ta ta wurin wanke ta da ruwa.

  8. sai ya cece mu, ba saboda abubuwan adalcin da muka aikata ba, sai dai saboda jinƙansa. Ya cece mu ta wurin wankan nan na sāke haihuwa da kuma sabuntawan nan ta Ruhu Mai Tsarki,