Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Vine

26 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Sa’an nan itatuwan suka ce wa kuringar inabi, ‘Ki zo ki zama sarkinmu.’

  2. “Amma kuringar ta ce, ‘In bar ruwan inabina, wanda yake faranta zuciyar alloli da mutane, in zo in yi fama da itatuwa?’

  3. Ka fitar da inabi daga Masar; ka kori al’ummai ka kuma dasa shi.

  4. Ka gyara wuri saboda shi, ya kuwa yi saiwa ya cike ƙasa.

  5. Aka rufe duwatsu da inuwarsa, manya-manyan itatuwan al’ul da rassansa.

  6. Ya miƙe rassansa zuwa Teku tohonsa har zuwa Kogi.

  7. Me ya sa ka rurrushe bangayensa don duk masu wucewa su tsinke ’ya’yan inabinsa?

  8. Aladu daga kurmi suna ɓarnatar da shi halittun gonaki kuma suna cinsa.

  9. Ka komo wurinmu, ya Allah Maɗaukaki! Ka duba daga sama ka gani! Ka lura da wannan inabi,

  10. Zan mai da ita kango, ba zan aske ta ba, ba kuwa zan nome ta ba, sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa kuwa za su yi girma a can Zan umarci gizagizai kada su yi ruwan sama a kanta.”

  11. Na shuka ka kamar zaɓaɓɓen inabi iri mai kyau da kuma wanda za a dogara a kai. Yaya kuma ka juya kana gāba da ni ka lalace, ka zama inabin jeji?

  12. ya kuwa yi toho ya zama kuringa gajeruwa mai yaɗuwa. Rassanta suka tanƙwasa wajen gaggafar, amma saiwoyinta suka zauna a ƙarƙashinta. Ta haka ta zama kuringa, ta yi rassa ta kuma fid da ganyaye.

  13. “ ‘Akwai kuma wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai da gashi mai yawa. Kuringan nan ta tanƙwasa saiwoyinta zuwa wajen wannan gaggafa daga inda aka shuka ta, ta kuma miƙe rassanta wajenta don gaggafar ta yi mata banruwa.

  14. An shuka ta a ƙasa mai kyau kusa da ruwa mai yawa don tă yi rassa masu yawa, ta ba da ’ya’ya ta kuma zama kuringa mai daraja.’

  15. “Ka gaya musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa wannan za tă ci gaba? Ba za a tumɓuke ta a kuma kakkaɓe ’ya’yanta don ta bushe ba? Dukan sababbin tohonta za su bushe. Ba sai da hannu mai ƙarfi, ko kuwa da yawan mutane za a tumɓuke ta daga saiwoyinta ba.

  16. Ko da an sāke shuka ta, za tă yi amfani ne? Ba za tă bushe gaba ɗaya sa’ad da iskar gabas ta hura ba, tă bushe a ƙasar da ta yi girma?’ ”

  17. “ ‘Mahaifiyarku kamar kuringa ce a cikin gonar inabi da aka shuka kusa da ruwa; ta ba da ’ya’ya da kuma cikakkun rassa saboda yalwan ruwa.

  18. Rassanta suka yi ƙarfi, suka dace da sandar mai mulki. Ta yi tsayi zuwa sama ana ganin ta saboda tsayinta da kuma saboda yawan rassanta.

  19. Amma aka tumɓuke ta cikin fushi aka jefar da ita a ƙasa. Iskar gabas ta sa ta yanƙwane, aka kakkaɓe ’ya’yanta; rassanta masu ƙarfi suka bushe wuta kuma ta cinye su.

  20. Yanzu an shuka ta a hamada, a busasshiyar ƙasa marar ruwa.

  21. Wuta ta fito daga jikin rassanta ta cinye ’ya’yanta. Babu sauran reshe mai ƙarfin da ya rage a kanta da ya dace da sandar mai mulki.’ Wannan waƙa ce kuma za a yi amfani da ita a matsayin makoki.”

  22. “Ni ne kuringar inabi na gaskiya, Ubana kuwa shi ne manomin.

  23. Yakan sare kowane reshe a cikina da ba ya ’ya’ya, amma yakan ƙundume kowane reshe da yake ba da ’ya’ya, domin yă ƙara ba da ’ya’ya.

  24. Kun riga kun zama masu tsabta saboda maganar da na yi muku.

  25. Ku kasance a cikina, ni kuma zan kasance a cikinku. Babu reshen da zai iya yin ’ya’ya da kansa, dole yă kasance a jikin kuringar inabin. Haka ku ma, ba za ku iya ba da ’ya’ya ba sai kun kasance a cikina.