Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Vine: Pruned

6 ayoyi · 5 fannoni

Ayoyi game da Pruned

  1. Zan mai da ita kango, ba zan aske ta ba, ba kuwa zan nome ta ba, sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa kuwa za su yi girma a can Zan umarci gizagizai kada su yi ruwan sama a kanta.”

  2. “Ni ne kuringar inabi na gaskiya, Ubana kuwa shi ne manomin.

  3. Yakan sare kowane reshe a cikina da ba ya ’ya’ya, amma yakan ƙundume kowane reshe da yake ba da ’ya’ya, domin yă ƙara ba da ’ya’ya.

  4. Kun riga kun zama masu tsabta saboda maganar da na yi muku.

  5. Ku kasance a cikina, ni kuma zan kasance a cikinku. Babu reshen da zai iya yin ’ya’ya da kansa, dole yă kasance a jikin kuringar inabin. Haka ku ma, ba za ku iya ba da ’ya’ya ba sai kun kasance a cikina.

  6. “Ni ne kuringar inabin; ku ne kuma rassan. In mutum ya kasance a cikina ni kuma a cikinsa, zai ba da ’ya’ya da yawa; in ba tare da ni ba, ba za ku iya yin kome ba.