Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tradition: Commandments of men

33 ayoyi · 3 fannoni

Ayoyi game da Commandments of men

Tace bisa littafi
  1. A lokacin nan Yesu ya bi ta gonakin hatsi a ranar Asabbaci. Almajiransa kuwa suna jin yunwa, sai suka fara kakkarya kan hatsi suna ci.

  2. Sa’ad da Farisiyawa suka ga wannan, sai suka ce masa, “Duba! Almajiranka suna yin abin da doka ta hana a yi a ranar Asabbaci.”

  3. Sai ya amsa ya ce, “Ba ku karanta abin da Dawuda ya yi ba ne sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa?

  4. Ya shiga gidan Allah, da shi da abokan tafiyarsa suka ci keɓaɓɓen burodin, wanda doka ta hana su yi, sai firistoci kaɗai.

  5. Ko kuwa ba ku karanta a Doka cewa a ranar Asabbaci firistoci sukan karya dokar Asabbaci duk da haka ba da yin wani laifi ba?

  6. Ina faɗa muku cewa waniwanda ya fi haikali yana a nan.

  7. Da a ce kun san abin da waɗannan kalmomi suke nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba,’da ba ku zargi marar laifi ba.

  8. Gama Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabbaci.”

  9. “Me ya sa almajiranka suke karya al’adun dattawa? Ba sa wanke hannuwansu kafin su ci abinci!”

  10. Yesu ya amsa ya ce, “Ku ma me ya sa kuke karya dokar Allah saboda al’adarku?

  11. Gama Allah ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,kuma duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole a kashe shi.’

  12. Amma ku kukan ce, in wani ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da dā ya kamata za ku samu daga gare ni an ba wa Allah,’

  13. ba zai ‘girmama mahaifinsa’ da shi ba. Ta haka kun yi banza da maganar Allah saboda al’adarku.

  14. (Farisiyawa da dukan Yahudawa ba sa cin abinci, sai sun wanke hannuwa sarai tukuna, yadda al’adun dattawa suka ce.

  15. Sa’ad da suka dawo daga wurin kasuwanci, dole su wanke hannu kafin su ci abinci. Sukan kuma kiyaye waɗansu al’adu da yawa, kamar wanken kwafuna, tuluna da butoci.)

  16. Saboda haka, Farisiyawa da malaman dokoki suka tambayi Yesu, suka ce, “Don me almajiranka ba sa bin al’adun dattawa, a maimakon haka suna cin abinci da hannuwa marasa tsabta?”

  17. Ya amsa ya ce, “Daidai ne Ishaya ya yi annabci game da ku munafukai; kamar yadda yake a rubuce cewa, “ ‘Waɗannan mutane da baki suke girmama ni, amma zukatansu sun yi nesa da ni.

  18. A banza suke mini sujada, koyarwarsu, dokokin mutane ne kawai.’

  19. Kun yar da umarnan Allah, kuna bin al’adun mutane.”

  20. Ya kuma ce musu, “Kuna da hanya mai sauƙi na ajiye umarnan Allah a gefe ɗaya, don ku kiyaye al’adunku!

  21. A wata ranar Asabbaci, Yesu yana bi ta gonakin hatsi, sai almajiran suka fara kakkarya kan hatsi suna murjewa a hannuwansu suna ci.

  22. Sai waɗansu Farisiyawa suka ce, “Me ya sa kuke yin abin da doka ta hana yi a ranar Asabbaci?”

  23. Yesu ya amsa musu ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi, sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa ba?

  24. Ya shiga gidan Allah, ya ɗauki keɓaɓɓen burodi, sa’an nan ya ci abin da firistoci kaɗai sukan ci bisa ga doka. Ya kuma ba wa abokan tafiyarsa?”

  25. Sai Yesu ya ce musu, “Ai, Ɗan Mutum ne Ubangijin Asabbaci.”