Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Tribe Of Gad: Land of, seized by the Moabites and Ammonites

7 ayoyi · 25 fannoni

Ayoyi game da Land of, seized by the Moabites and Ammonites

  1. “Sauko daga darajarku ku zauna a busasshiyar ƙasa, Ya mazaunan Diyar Dibon, gama shi mai hallaka Mowab zai haura a kanku zai kuma lalace biranenku masu kagarai.

  2. Ku tsaya a bakin hanya ku duba, ku da kuke zama a Arower. Ku tambayi mutumin da yake gudu da macen da take tserewa, tambaye su, ‘Me ya faru?’

  3. An kunyata Mowab, gama ta wargaje. Ku yi kuka ku kuma tā da murya! Ku yi shela kusa da Arnon cewa an hallaka Mowab.

  4. Hukunci ya zo wa tudu, zuwa Holon, Yahza da Mefa’at,

  5. zuwa Dibon, Nebo da Bet-Dibilatayim,

  6. zuwa Kiriyatayim, Bet-Gamul da Bet-Meyon,

  7. zuwa Keriyot da Bozra zuwa dukan garuruwan Mowab, nesa da kusa.