Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Lot

34 ayoyi · 9 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Haruna zai jefa ƙuri’a don awaki biyun ɗin, ƙuri’a ɗaya domin Ubangiji, ɗayan kuma don azazel

  2. Haruna zai kawo akuyar da ƙuri’a ta fāɗi a kai wa Ubangiji yă miƙa ta na hadaya don zunubi.

  3. Amma za a miƙa akuyar da aka zaɓa ta wurin ƙuri’a a matsayi ta azazel da rai a gaban Ubangiji don a yi amfani da ita don kafara ta wurin korinta zuwa cikin jeji kamar azazel.

  4. Sa’ad da Sama’ila ya kawo dukan Isra’ila gaba, kabila-kabila, sai aka zaɓi kabilar Benyamin ta wurin jefa ƙuri’a.

  5. Sai ya kawo kabilar Benyamin gaba, iyali-iyali, aka zaɓi iyalin Matri. A ƙarshe aka zaɓi Shawulu ɗan Kish. Amma da aka neme shi sai ba a same shi ba.

  6. Aka karkasa su babu sonkai ta wurin jifa ƙuri’a, gama akwai manyan ma’aikatan wuri mai tsarki da manyan ma’aikatan Allah a cikin zuriyar Eleyazar da Itamar.

  7. Shemahiya ɗan Netanel, wani Balawe ne marubuci, ya rubuta sunayensu a gaban sarki da kuma a gaban manyan ma’aikata. Zadok firist, Ahimelek ɗan Abiyatar da kuma kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa, iyali guda daga Eleyazar, guda kuma daga Itamar.

  8. Ƙuri’a ta farko ta faɗa a kan Yehoyarib, na biyu a kan Yedahiya,

  9. na uku a kan Harim, na huɗu a kan Seyorim,

  10. na biyar a kan Malkiya, na shida a kan Miyamin,

  11. na bakwai a kan Hakkoz, na takwas a kan Abiya,

  12. na tara a kan Yeshuwa, na goma a kan Shekaniya,

  13. na goma sha ɗaya a kan Eliyashib, na goma sha biyu a kan Yakim,

  14. na goma sha uku a kan Huffa, na goma sha huɗu a kan Yeshebeyab,

  15. na goma sha biyar a kan Bilga, na goma sha shida a kan Immer,

  16. na goma sha shida a kan Hezir, na goma sha takwas a kan Haffizzez,

  17. na goma sha tara a kan Fetahahiya, na ashirin a kan Ezekiyel,

  18. na ashirin da ɗaya wa Yakin, na ashirin da biyu a kan Gamul,

  19. na ashirin da uku wa Delahiya da kuma na ashirin da huɗu a kan Ma’aziya.

  20. Ga tsarin aikinsu na hidima sa’ad da suka shiga haikalin Ubangiji, bisa ga ƙa’idar da kakansu Haruna ya kafa, yadda Ubangiji, Allah na Isra’ila ya umarce shi.

  21. Game da sauran zuriyar Lawi kuwa, Daga ’ya’yan Amram maza. Shubayel; daga ’ya’yan Shubayel maza. Yedehiya.

  22. Game da Rehabiya kuwa, daga ’ya’yansa maza. Isshiya shi ne na fari.

  23. Daga mutanen Izhar, Shelomot; daga ’ya’yan Shelomot maza, Yahat.

  24. ’Ya’yan Hebron maza su ne, Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu.

  25. Ɗan Uzziyel shi ne, Mika; daga ’ya’yan Mika maza, Shamir.