Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Lot

34 ayoyi · 9 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ɗan’uwan Mika shi ne, Isshiya; daga ’ya’yan Isshiya maza, Zakariya.

  2. ’Ya’yan Merari su ne, Mali da Mushi. Ɗan Ya’aziya shi ne, Beno.

  3. ’Ya’yan Merari su ne, daga Ya’aziya, Beno, Shoham, Zakkur da Ibri.

  4. Daga Mali, Eleyazar, wanda ba shi da ’ya’ya maza.

  5. Daga Kish, ɗan Kish shi ne, Yerameyel.

  6. Kuma ’ya’yan Mushi maza su ne, Mali, Eder da Yerimot. Waɗannan su ne Lawiyawa bisa ga iyalansu.

  7. Suka kuma jifa ƙuri’a, kamar dai yadda ’yan’uwansu zuriyar Haruna suka yi, a gaban Sarki Dawuda da gaban Zadok, Ahimelek, da kuma a gaban kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa. Aka yi da iyalan wa daidai da iyalan ƙane.

  8. Da sojojin suka gicciye Yesu, sai suka ɗibi tufafinsa suka kasa kashi huɗu, kowanne ya ɗauki kashi ɗaya. Suka kuma ɗauki taguwarsa, taguwar kuwa ba ɗinki, saƙa ɗaya ce gudanta daga sama har ƙasa.

  9. Sai suka ce wa juna, “Kada mu yage ta, sai dai mu jefa ƙuri’a a kanta mu ga wanda zai ci.” Wannan ya faru ne don a cika nassin da ya ce, “Suka rarraba tufafina a junansu, suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigata.” Abin da sojojin suka yi ke nan.