Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Feast of the Passover: Purification necessary to the due observance of

5 ayoyi · 43 fannoni

Ayoyi game da Purification necessary to the due observance of

  1. Suka yanka ɗan ragon Bikin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu na wata na biyu. Firistoci da Lawiyawa suka ji kunya suka tsarkake kansu, suka kawo hadayun ƙonawa a haikalin Ubangiji.

  2. Sa’an nan suka ɗauki matsayinsu na kullum yadda yake a Dokar Musa mutumin Allah. Firistoci suka yayyafa jinin da Lawiyawa suka ba su.

  3. Da yake da yawa cikin taron ba su tsarkake kansu ba, dole Lawiyawa su yanka ’yan ragunan Bikin Ƙetarewa domin dukan waɗanda ba su da tsarki, ba su kuma iya tsarkake ragunansu ga Ubangiji ba.

  4. Ko da yake yawancin mutanen da suka zo daga Efraim, Manasse, Issakar da Zebulun ba su tsarkake kansu ba, duk da haka suka ci Bikin Ƙetarewa, ba tare da bin abin da yake a rubuce ba. Amma Hezekiya ya yi addu’a dominsu cewa, “Bari Ubangiji, wanda yake nagari, yă gafarta wa kowa

  5. wanda ya sa zuciyarsa ga neman Allah, Ubangiji Allah na kakanninsa, ko da shi marar tsarki ne bisa ga dokokin wuri mai tsarki.”