Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Feast of the Passover: Sacrifices during

6 ayoyi · 43 fannoni

Ayoyi game da Sacrifices during

  1. Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimai biyu, rago ɗaya, da ’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya; dukansu kuma marasa lahani ga Ubangiji.

  2. Da kowane bijimi, a shirya kashi ɗaya bisa uku na efan lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai; da rago guda kuwa, a shirya kashi biyu bisa goma na efan lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai;

  3. da kowane ’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma.

  4. A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, don yin muku kafara.

  5. Ku shirya wannan tare da hadaya ta ƙonawa ta kowace safiya.

  6. Ta haka za a shirya abinci don hadayar da aka yi da wuta, kowace rana, har kwana bakwai don daɗin ƙanshi ga Ubangiji; a shirya shi haɗe da hadaya ta ƙonawa ta kullum, da kuma hadaya ta sha.