Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Terah

11 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Sa’ad da Nahor ya yi shekaru 29, sai ya haifi Tera.

  2. Bayan ya haifi Tera, Nahor ya yi shekara 119, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

  3. Bayan Tera ya yi shekaru 70, sai ya haifi Abram, Nahor da Haran.

  4. Wannan ita ce zuriyar Tera. Tera ya haifi Abram, Nahor da Haran. Haran kuma ya haifi Lot.

  5. Yayinda mahaifinsa Tera yana da rai, Haran ya rasu a Ur ta Kaldiyawa, a ƙasar haihuwarsa.

  6. Abram da Nahor suka yi aure. Sunan matar Abram, Saira ne, sunan matar Nahor kuwa Milka; ita ’yar Haran ce, mahaifin Milka da Iska.

  7. Saira kuwa bakararriya ce, ba ta da yara.

  8. Tera ya ɗauki ɗansa Abraham, jikansa Lot ɗan Haran, da surukarsa Saira, matar Abram, tare kuwa suka bar Ur ta Kaldiyawa, don su tafi Kan’ana. Amma sa’ad da suka zo Haran sai suka zauna a can.

  9. Tera yi shekaru 205, ya kuma mutu a Haran.

  10. Yoshuwa ya ce wa dukan mutanen, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Dā can, kakanninku, Tera mahaifin Ibrahim, da Nahor sun zauna a hayin Kogin Yuferites suka yi wa waɗansu alloli sujada.

  11. ɗan Yaƙub, ɗan Ishaku, ɗan Ibrahim, ɗan Tera, ɗan Nahor,