Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sin Offering

61 ayoyi · 25 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Amma Habila ya kawo mafi kyau daga ’ya’yan fari na garkensa. Ubangiji ya yi farin ciki da sadakar da Habila ya kawo,

  2. Da ka yi abin da yake daidai, ai, da ka sami karɓuwa. Amma tun da ba ka yi abin da ba daidai ba, zunubi zai yi fakonka don yă rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so yă mallake ka, amma tilas ka rinjaye shi.”

  3. “Ka kuma kawo bijimin a gaban Tentin Sujada, sai Haruna da ’ya’yansa su ɗora hannuwansu a kansa.

  4. Amma ka ƙone naman bijimin, da fatarsa, da kayan cikin, a bayan sansani. Hadaya ce ta zunubi.

  5. “Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Sa’ad da wani ya yi zunubi ba da gangan ba, har ya karya ɗaya daga cikin dokokin Ubangiji,

  6. “ ‘In shafaffen firist ya yi zunubi, ya jawo wa jama’a laifi, dole yă kawo wa Ubangiji ɗan bijimi marar lahani a matsayin hadaya don zunubi saboda zunubin da ya yi.

  7. Zai kawo bijimin a ƙofar Tentin Sujada a gaban Ubangiji. Zai ɗibiya hannunsa a kan bijimin, yă kuma yanka shi a gaban Ubangiji.

  8. Sa’an nan shafaffen firist zai ɗiba jinin bijimin yă kai cikin Tentin Sujada.

  9. Yă tsoma yatsarsa a cikin jinin, yă kuma yafa sau bakwai a gaban Ubangiji, a gaban labulen wuri mai tsarki.

  10. Sa’an nan firist ɗin zai zuba jinin a ƙahonin bagaden turare masu ƙanshi da suke a gaban Ubangiji a Tentin Sujada. Sauran jinin bijimin zai zuba a gindin bagaden hadaya ta ƙonawa a ƙofar zuwa Tentin Sujada.

  11. Zai cire dukan kitsen daga bijimin hadaya don zunubi, kitsen da ya rufe kayan cikin, ko kuwa da suka shafe su,

  12. da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta, waɗanda zai cire tare da ƙodoji.

  13. Zai cire su daidai kamar yadda akan cire na bijimin hadaya ta salama. Sai firist ɗin yă ƙone su a kan bagaden ƙona hadaya.

  14. Amma fatar ɗan bijimin, da namansa, da kansa, da ƙafafunsa, da kayan cikinsa, da hanjinsa,

  15. wato, dukan sauran bijimi, dole yă ɗauke su zuwa waje da sansani zuwa wani wuri mai tsabta inda ake zub da toka, yă ƙone shi a itacen da yake cin wuta a tarin toka.

  16. “ ‘In dukan jama’ar Isra’ilawa suka yi zunubi ba da gangan ba, har suka aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, ko da yake jama’ar ba su san batun ba, duk da haka sun yi laifi.

  17. Sa’ad da suka gane da zunubin da suka aikata, dole taron su kawo ɗan bijimi a matsayin hadaya don zunubi, su kawo shi a gaban Tentin Sujada.

  18. Dattawan jama’a za su ɗibiya hannuwansu a kan bijimin a gaban Ubangiji, sai a yanka bijimin a gaban Ubangiji.

  19. Sa’an nan shafaffen firist zai ɗibi jinin bijimi zuwa cikin Tentin Sujada.

  20. Zai tsoma yatsarsa cikin jini yă kuma yayyafa shi a gaban Ubangiji sau bakwai a gaban labule.

  21. Zai cire dukan kitsen daga gare shi yă ƙone a kan bagade,

  22. Sa’an nan zai ɗauki bijimin waje da sansani yă ƙone shi kamar yadda ya ƙone bijimi na fari. Wannan ita ce hadaya don zunubi domin jama’a.

  23. “ ‘Sa’ad da shugaba ya yi zunubi ba da gangan ba, har ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji Allahnsa ya umarta, to, ya yi laifi.

  24. Sa’ad da aka sanar da shi game da zunubin da ya yi, dole yă kawo bunsuru marar lahani a matsayin hadayarsa.

  25. Zai ɗibiya hannunsa a kan bunsurun yă kuma yanka shi a inda ake yankan hadayar ƙonawa a gaban Ubangiji. Hadaya ce ta zunubi.